Alhamdulillahi!!! Ga Wani Taimako Daga Allah ; Amurika Ta Aminta Da Sayarwa Da Nigeria Jirgin Yaki (Hotuna)
Gwamnatin Nigeria ta dauki tsawon lokaci tun a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tana rokon Amurka da ta sayar mata da jirgin yaki marar matuki (Drone) amma Amurka taki amincewa, saboda wasu dalilai da sharadi wanda Nigeria ta kasa cikawa
Alhamdulillah yanzu haka shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya amince Kasarsa zata sayar wa Nigeria wannan jirgi na yaki albarkacin nagarta da kuma gaskiyar shugaba Buhari Maigaskiya, ba wai don Nigeria ta kammala cika sharadin ba
Wannan makamin idan Nigeria ta mallakeshi to batun wai Boko Haram su fito suyi zuga su kaddamar da harin ta’addanci a wani gari ko sansanin sojoji ko su tare hanya suyi ta’addanci su koma jeji kalau ya kare da taimakon Allah
Jirgin yana gudu kamar iska, zai iya tashi daga Lagos ya isa Borno a mintuna kalilan, wato na kwatanta mana tsawon Nigeria kenan gabas da yamma, sannan daga Lagos za’a iya sarrafa jirgin ba tare da matuki ba, jirgin yaje yayi ruwan bama-bamai akan Boko Haram ya dawo
Sannan jirgi ne na leken asiri wanda yake dauke da manyan kamarori da na’urar daukan hoto da bidiyo, zai iya bacewa a sararin samaniya, wanda yake kasa ko ya daga kai ba zai iya hangensa ba, amma shi jirgin zai iya zooming ya gano abinda yake kasa, har yayi aiming wato saiti ya harba makami, jirgin yana daukar makamai masu linzami
Da irin wannan jirgin Amurka ta gano maboyar Shugaban kungiyar Al-Qaedah Osama bin Laden tayi hari ta kashe shi, da jirgin ta gano maboyar shugaban ISIS Abubakar Al-baghdadi wanda ya tarwatsa kansa da bomb, da irin wannan jirgi tayi harin da ya hallaka shugaban sojojin ta’addanci na Kasar Iran Qassem Suleimani, Amurka ta gano manyan gawurtattun ‘yan ta’addan da irin wannan jirgi ta kuma kashe su
Muna rokon Allah Ya sa da irin wannna jirgi za’a hallaka shugabannin kungiyar Boko Haram gaba dayansu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.
Daga: Datti Assalafy