A shirye mu ke mu farfado da Kannywood – Lawal Ahmad
Jarumi a masana’antar Kannywood, Lawal Ahmad wanda ya kasance mataimakin shugaban kungiyar Arewa Film Makers Association ta kasa reshen jihar Kano, ya tabbatar da cewa babban kudurin sa a yanzu shi ne ya ga martabar masana’antar Kannywood ta dawo da kimar ta kamar yadda ta ke a can baya.
Jarumi Lawal Ahmad, ya fadi haka ne a yayin tattaunawar da ya yi da wakiliyar mu a kan abubuwan da su ka shafi masana’antar Kannywood.
Wakiliyar ta mu ta fara tambayar sa kamar haka:
Kwana biyu ka dage da yin fim mai dogon zango, maimakon fim na lokaci guda wanda ka saba yi a baya ko menene dalilin hakan kuwa a wajen ka?
“Yanzu zamani ne ya canja, domin duk wani fim mai nishadantar da duniya, amfi mayar da hankali a kan mai dogon zango wato Series yanzu, tun daga kan Hollywood da Bollywood da dai sauran masana’antar shirya fina-finai, wannan dalilin ya sa har Kannywood mu ka koma zuwa yin fim din Series”.
Amma da yawa a na ganin kamar yanayin kasuwancin masana’antar na wani mawuyacin hali, me ya sa a ka koma ga yin fim din Series din, kuma a ka saka shi a YouTube?
“Eh to gaskiya da hakan ma, domin yanzu idan ki ka duba za ki ga kasuwar cd da DVD ta yi kasa yanzu, yawancin fina-finan Online wato Internet a ke kallo na YouTube da kuma manhajoji kenan, ina nufin komai ya koma Digital, domin haka dole sai dai a yi fim mai dogon zango ko kuma a yi fim a saka a manhajoji”.
Amma ta ya ya ka ke ganin kasuwancin fina-finan a yanzu?
“Alhamdulillahi, gaskiya kawai zance idan wata hanyar ta bude, Allah zai bude wata, domin haka a kan wannan gabar sai dai kawai na ce Alhamdulillahi, domin gaskiya a harkar nan ta YouTube kasuwanci ne wanda duk mutumin da zai yi shi to dole sai ya zuba jari, sannan kuma a hankali ya ga ribar abun, sabanin wancan na CD da ya zamana fim din ma mutum sai ya karbi bashi sai ka jira ya buga ya siyar, sannan ya biya ka kudin ko kuma ma ya baka rabin kudin, domin haka gaskiya mu babu abun da zamu ce sai dai Alhamdulillahi kawai”.
Wannan ya na nufin a na ka ganin kasuwancin fina-finai a YouTube da manhajoji ci gaba ne kenan a masana’antar?
“Babba ma kuwa gaskiya, domin inda ba ci gaba ba ne ba kuma babu wani abu da za mu mora a ciki, kuma ci gaba ne mai dorewa, sannan kuma da mutane basu raja’a a kan sa ba. Saboda haka ni a gani na ci gaba ne gaskiya, saboda idan ka yi wanda za a kalla din za a kalla, idan ka ga ba a kalla ba to ba ka yi wanda za a kalla din ba”.
Akwai wata tattaunawa da na ga anyi da kai a kwankin baya da ka ke cewa, Kannywood ta yi mu ku komai, kuma a shirye ku ke domin ganin kun farfado da ita tare da dawo da martabar ta, shin wane gudunmawa ka ke da burin bayar wa, domin ganin martabar masana’antar ta daidaita kamar yadda ka fada?
“Yanzu haka ni ne mataimaki na kungiyar Filmmakers Association, kuma wannan harkar ta YouTube din ta na daga cikin abubuwan da mu ke son mu kirkira, saboda harkar Corona ce ta sa komai ya tsaya, har ta kai ba mu yi nisa ba gaskiya. Amma dai Insha Allah ya na daya daga cikin abubuwan da za mu haskawa jama’a, mu nuna mu su yadda harkar ta ke, kasancewar mu shuwagabanni mu zo mu yi kokari a kai, tun da kowa hanyar da zai fita ya ke nema, domin haka gaskiya wannan harkar ta YouTube din ta na daya daga cikin abubuwan da za mu yi, tun da dama akwai Sinima, akwai gidajen TV a na yi, duk kuma su na karba. Domin haka yanzu abu na gaba shi ne mu wayarwa mutane kai kan YouTube Channels da Manhajoji, wannan shi ne kawai“. A cewar Lawal Ahmad. Northflix na ruwaito.