Uncategorized

Za ki Burge Mijinki Kawai Da Abun Da Ya Fi So Wani Sirri Zuwa Ga Matan Aure – Daga Real Fauziyya D. Sulaiman

Watarana wata na bani labarin cewa; Shekararsu Ashirin da uku da mijinta da yaransu biyar, sai su ka dan samu sabani rannan sai ta ke baiwa wata sabuwar makociyarta da su ka dawo, ta ce kwana biyu ko abincinta ba ya ci, sai makociyar ta ce ma ta zan baki wasu Riga da Wando ki tsuke da ya shigo ki rungume shi kina darling sannu da zuwa, ina me tabbatar miki kin gama da shi, haka na ke yiwa mijina, ta ce kuwa haka aka yi, sai dai maimakon ta samu abun da kawarta ta gaya Mata sai sabanin haka, don hatta yayanta tsayawa su ka yi suna kallonta da mamaki, shi kuma mijin har kararta ya kai gidansu wai tafi karfinsa, da kyar aka sasanta lamarin.

Don haka ki fahimci abin da mijinki ya fi so shine babban makamin zaman lafiyarki, wani baya son yawan magana wani yan so, wani miskiline wani mai haba-haba ne, wani mai taurin kai ne, wani yana da saukin kai, wani mai fada ne wani mai sanyi ne, wani mai kyauta ne wani mai rowa ne, wani mai san nishadi ne, wani mai tsare gidana ne, don haka gane waye shi ki iya zama da shi, shine za ki ji ana cewa wane miskilile amma tsoron wance  ya  ke, ko ita kadai ya ke yiwa dariya, don haka aikin da ke gabanku mata fahimtar wa ki ke aure.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button