‘Yan fim a koma makaranta a yi karatu – Tijjani Usman Faraga
Daya daga cikin jarumai da ya dade a na damawa da shi a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, Tijjani Usman Faraga, ya yi kira ga abokan sana’ar sa ma su harkar fim da su yi amfani da irin darusan da su ka samu a lokacin da a ka yi zaman kullen Covid-19.
Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu kan irin darasin da ya kamata a ce ‘yan fim sun dauka daga yanayin zaman gida da a ka yi dangane da cutar Covid-19.
Da farko ya fara da cewar “Tun farko ma idan na duba yadda mu ka samu kan mu a harkar fim a can baya lokacin da mu ka taso, a kwai bambanci da yadda a ke gudanar da ita a wannan lokacin, domin a can baya da farko duk wanda ya shigo harkar, to ya na da kishin masana’antar, to sai dai kuma a yanzu saboda yanayin canjin abubuwa da a ka samu na zamani, sai abubuwan su ka canza da ya yadda a ke yi a can baya. Misali, ka ga a baya fim din ma a kaset a ke saka shi, sai a ka ci gaba a ka dawo CD a ka koma DVD, yayin da a yanzu kuma abun ya kara ci gaba zuwa online YouTube da sauran abubuwa na online, to a daidai lokacin da a ka fara tunanin yadda za a yi a gyara harkar sai kuma matsalar Covid-19 ta bullo, wanda ya tsayar da komai hakan ya sa ita kanta uwar kungiyar ma su gudanar da harkokin sana’ar fim ta kasa MOPPAN su ka dakatar da duk wani aiki da ya shafi harkar fim, wanda har zuwa yanzu ba a dawo gaba daya ba, domin haka masana’antar har yanzu ba ta fara tsayawa da kanta ba, saboda haka sai dan abun da ba a rasa ba wanda a ke yi”.
Ko wanne darasi ‘yan fim su ka samu dangane da halin da a ka samu kai na zama babu aiki?
“E to irin wannan abun daman idan ya bullo mutum tunani zai yi, ya ga yaya sanar sa za ta kasance, domin haka yanzu abun da ya kamata a yi a wannan masana’antar, shi ne mu hada kai da Gwamnati yadda za mu samu ta rinka jin kukan mu, yadda duk abubuwan da mu ke yi ya kasance ta shigo ta ba mu karfin gwiwa, domin haka kai da ka ke yi ka samu kwarin gwiwa na ci gaba da yin aikin.
Misali sanin ilimin yadda a ke gudanar da aikin cikin ilimi, idan mu na da wannan, to idan wani abu ya taso irin wannan Annobar ta Covid-19, to ya san yadda zai ya kare kan sa kafin a samu mafita, domin haka ilimin sanin hakan ya na da muhimanci, saboda haka babu wata masana’antar da za a yi ta har ta dore ba tare da an je an nemo ilimin ta ba, wannan ya sa idan wata Annoba ta zo sai ya zama mutane ba su san ma ina za su sa gaban su ba, domin haka ina kira ga ‘yan fim da cewar gaskiya a koma a yi karatu, domin idan ka kula wadanda su ka yi ilimin a yanzu za ka ga su ne su ka fi yin fice a cikin masana’antar kuma su ke gudanar da ita, duk duniya su a ke kallo, saboda mai daki shi yasan inda ruwa yake yi masa yoyo, domin haka duk wanda zai ci gaba da harkar to ya san cewar ilimin sa ne zai sa ya samu dama da yawa a cikin masana’antar. Haka zalika mu bude tunanin mu domin samar wa ita masana’antar ‘yanci da kuma girmama ta”. Inji Faraga.
Tijjani Usman Faraga ya kuma yii fatan alheri ga dumbin masoyan sa da a kullum su ke nuna masa kauna a duk lokacin da su ka hadu. Northflix na ruwaito.