Yadda Wani Abu Mai Fashewa Da Ake Tsamin Bam ne Ya Kashe Kananan Yara Bakwai Ya Jikkata Biyar A Katsina (Hotuna)
…’yan sanda sun ceto wadanda ‘yan bindiga suka sace su 14 a daren jiya
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Da safiyar yau ne, wane abu mai fashewa, wanda ake kyautata tsammanin Bam ne, ya fashe a garin ‘Yanmama da ke cikin karamar hukumar Malumfashi, inda ya kashe kananan yara bakwai har lahira da kuma jikkata biyar da suka je wata gona domin yin ciyawa.
Wani mazaunin garin ‘Yanmama, wanda bai so a ambaci sunan sa ya shaidawa RARIYA ta waya cewa kananan yara ne, su goma sha biyu, sun je yin ciyawar da za su ba dabbobin su, sai wani abun fashewa ya fashe a gonar nan take yara bakwai suka rasu, guda biyar kuma an tafi da su asibitin garin Malumfashi, sanadiyyar raunuka da suka samu daban-daban. Yanzu haka jami’an tsaro sun zo wurin sun kuma killace gonar.
A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar ceto wasu mutane goma sha hudu, da yan bindigar suka sace a daren jiya, a garin Kwantamawa da ke cikin karamar hukumar Dutsinma.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takardar manema labarai da Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya rabawa manema labarai a Katsina. Inda ya ce da Misalin karfe dayan daren jiya Juma’a ne, yan bindigar sama da arba’in, bisa babura dauke da bindigogi kirar AK47 suka kai hari a garin Kwantamawa da ke karamar hukumar Dutsinma, inda suka sace mata da kananan yara goma sha hudu da shanu talatin da kuma tumakai sittin a garin. Baturen yan sanda na Dutsinma ya jagoranci wata tawagar jami’an tsaro, inda suka yi ba ta kashi da su, har suka yi nasarar kubutar da wadanda suka sace da kuma kafatanin dabbobin da suka sace. Kuma sun yi nasarar cafke wani daga cikin yan bindigar mai suna Amadu Yusuf, dan shekara talatin da haihuwa, da ke garin Tudu a Karamar Hukumar Dutsinma.
Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah ya ce yanzu haka rundunar na ci gaba da bincike abinda ya fashe a Yarmama da kuma harin da yan bindigar suka a garin Kwantamawa da kuma Zamfarawa a Karamar Hukumar Batsari a daren jiya.