Yadda Gasar Manyan Mata Ta Gudana Da Bayar Da Kyauta Ga Waɗanda Nayi Nasara
A jiya Lahadi, 12 ga watan Yuli aka gudanar da bada kyaututtuka ga wadanda su ka yi nasarar lashe gasar sabon fim din nan mai suna Manyan Mata, wanda kamfanin Abnur Entertainment, za su fara shiryawa a wata mai kamawa.
A watan da ya gabata ne dai kamfanin suka sanya gasar, inda suka tsara mabambantan tambayoyi guda biyar, tare da alkawarin bada kyaututtuka ga mutane biyar wadanda suka amsa tambayoyin da su ka tsara.
A cikin tambayoyin da suka tsara sun bukaci a Lissafa sunan jarumai mata goma 11 na jikin fastar da za su saki, wanda za su fito cikin fim din Manyan Mata. Sannan sun kara bukatar a lissafa sunan jarumai guda biyar Maza wanda za su fito cikin fim din.
Haka zalika sun tambayi cewa mutum nawa ne za su ba da umarni cikin fim din, wata tambayar kuma ita ce, marubuta nawa ne suka rubuta fim din Manyan Mata? Suka kuma ce a Lissafo su. Tambaya ta karshe a cikin tambayoyin ita ce wanene furodusan Manyan Mata kuma wadanne garuwa ne za a daukar shirin.
Mutane sama da 400 sun fafata a shafin Instagram inda anan ne wurin da ka ware domin bada amsoshin.
Abubakar A. Hassan wani matashi dan shekara 15 mazaunin garin Kaduna, shi ne wanda ya zo na daya gasar, inda ya yi nasarar samun kyautar matsakaiciyar na’ura mai kwakwalwa da kudi naira dubu biyar.
Farida Ahmad Ibrahim Mafara, ce ta zo ta biyu inda ta samu nasarar lashe waya kirar ”Techno Spark 4″ da kuma Materials guda biyu sai turaren wuta guda biyu na kamfanin… sai kudi naira dubu biyar.
Sai kuma Habiba Abdullahi, wadda ita ce tazo na uku a gasar, inda ta samu kyautar shadda kirar “Getzner” da kuma naira dubu biyar
Khalil Yusuf ATA shi ne ya zo na hudu, inda shi kuma ya samu nasarar lashe shadda “Getzner” da kuma naira dubu biyar
Sai kuma Fatima Yusuf, wadda ita ce tazo na biyar a manyan rukunin farko, inda ta samu nasarar Atamfa “Super Wax” da kuma naira dubu biyar.
Shi dai fim din Manyan Mata fim ne da za a shirya don katange mata daga fyade da cin zarafin ƙananan yara. Haka zalika akwai Sako na musamman a cikin sa game da yadda za a cire matan aure daga ƙangin bauta, da kuma