Uncategorized

Yadda Fushi Ga Mace Mai Ciki Ke Cutar Da Kwakwalwar Jariri

By Idris Aliyu Daudawa

Wani likita a jami’ar Wayne dake Boston ta kasar Amurka mai suna Moriah Thomason ya bayyana cewar yawan yin fushi ko kuma wata damuwa ga mace mai ciki na da matukar illa sosai ga abin dake cikin ta saboda hakan na hana kwakwalwar abin yin girma kamar dai yadda ya kamata.

Thomason ya gane hakan ne bayan wani binciken da ya gudanar akan yanayin girman jaririn dake cikin Iyayen su mata.

Ya ci gaba da bayanin cewar “A shekarun baya idan ba a manta ba wasu likitoci sun bayyana illolin da suke tattare da yin fushi ko kuma damuwa ga mai ciki, amma kuma saboda basu tabbatar da hakan ba, mutane masu yawa sun dauka wani canfi ne wanda ya sa na gudanar da wannan bincike don gano ainihin gaskiyar maganar.”

Ya ci gaba da yi shi bayani akan shi binciken daya gabatar ne akan wasu mata 47 masu cikin wata takwas da wata tara, daga nan kuma sai ya zabo su daga wureren da mutane suka fi fama da matsalolin halin rayuwa ta yau da kullun.

Thomason ya yi wani karin haske inda kuma yace binciken ya nuna cewa sanadiyyar damuwa na halin rayuwar yau da kullun da kuma yawan fushi da wadannan mata ke fama da shi ya hana lalata kwakwalwar ‘ya’yan dake cikin su yin girma kamar dai yadda ya kamata.

Saboda hakan nema yake kira ma musamman ga mata masu ciki da su yi kokari su rage yawan damuwa da yin fushi domin kaucewa haihuwar ‘y’ya wadanda na iya kasancewa musakai ne.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button