Kannywood

Wakar Jarumar Mata Mallakina Ce ~ Darakta Sanusi Oscar 442

Advertisment

Mai bada umari a masana’antar Kannywood da shirya wakoki, Sunusi Oscar 442 ya ce nasarorin da wakar jaruma mata ta samu babban nasara ne a gare shi sakamakon yadda wakar ta yi tashe musamman ma a lokacin lockdown.

Cikin wata tattaunawa da Northflix ta yi da fitaccen mai bada umarni a fina-finai da kuma wakoki a masana’antar Kannywood din wato Sunusi Oscar 442, dangane da nasarar da wakar sa ta jarumar mata ta yi, inda ya ke cewa ba a iya nasarar wakar jarumar mata ta tsaya ba, har ma da duniy baki daya.

Northflix ta tattauna da shi kamar haka:
Kasancewar ka darakta a masana’antar Kannywood kuma ka ke bada umarni a wakoki da kuma fina-finai, wanne yafi burge ka kafi jindadin yi a cikin su?

“Kasancewa ta darakta wanda na ke yin hannu biyu wato na ke cin tudu biyu, duk kan su ina son su, saboda aiki na ne kuma duk wanda ya baka aiki ya na son ya ga ka yi masa yadda yakamata. Kuma kafin na fara daraktin waka fim na fara, sannan sai an kware a fim a ke iya daukar waka, domin haka kwarewa ce ta saka nake daraktin wakoki”.

Advertisment

Kuma akwai waka da ka yi daraktin wadda ta zama zakaran gwajin dafi a ciki da wajen Kannywood mai suna jarumar mata wadda a ka yaba a ko ina, ya ka ji a zuciyar ka game da wannan nasara da ka samu?

“Gaskiya ne waka ta ta jarumar mata ta samu nasara sosai saboda ni ne na saye ta, sannan jajircewa da mu ka yi shi ya sa wannan waka ta samu nasara, sau da yawa mutane su kan bada waka amma wani idan ka ce masa za a kashe kudi sai ya rinka jin kamar ko wasa ne ko ma abun ba zai yi wu ba, to ikon Allah ita wannan waka mallaki nace, ni na siye ta na biya kudin ta na dauki nauyin ta kuma na yi ta a garuruwa guda uku, Kano, Abuja da kuma Bauchi, kuma hakan ya taimaka wajen samar da abun da a ke so da kuma nasarar da a ka samu yanzu haka”.

Wane ci gaba ka ke son ka kara kawo wa nan gaba a wakokin ka, domin ganin ci gaban su an yi aiki mai kyau?

“Maganar gaskiya Ina son na samu ci gaba, na kuma kawo ci gaban da Afrika babu wanda ya ke da ci gaba irin wannan a matsayi na a darakta na fim da na waka baki daya, abun nasara ne kuma ci gaba  ne a ce an samu fitaccen darakta wanda ya ke kafada-kafada da irin su nahiyar Turai da yankin Asiyaa da sauran su, ina fatan haka ba na jin a raina cewa bazan kai hakan ba in dai mu na raye, domin ba buri na Kannywood ba, ba shine buri na ba, shi ya sa ba na cikin mutanen da su ke da rijista da jihar Kano, amma dani da mutane na su na bamu hadin kai, domin ba sai da kano a ke ci gaba a idanun duniya ba, kuma ba sai da Kano a ke ci gaba a rayuwar duniya ba, ni bukata ta in zama mai harkoki a duniya, ba a cikin gida ba ko a jihar Kano ba shi ne buri na ba, domin haka na dai na yin fim a Kano, hakan bazai hana ni ci gaba ba, duk inda na ke son na je na yi zan yi, muddin ka yadda da abun da ka ke yi kuma ka dogara da Allah to Allah zai baka nasara”.

An samu sau yi kuma a masana’antar fina-finai ta Kannywood daga kasuwa zuwa internet, wane ci gaba ka ke ganin masana’antar ta samu ta wannan bangaren?

“Sauye-sauyen da a ka samu ai su na da yawa, masana’antar Kannywood da take kasuwa ta na hannun mutane guda biyu, da Ali Nnuhu da kuma Adam Zango, wadannan su a ke kai fim din su kasuwa a ce sai su, idan mutum ya yi fim idan ba su ba, ko ya kai kasuwa baza a siya ba, duk kyawun fim din ka da kuma kyawun labarin ka da iya tsarawa, sannan da karfin kamfanin ka in dai ba su ne a fim din ka ba, sai fim din ka ya wulakan ta, to amma yanzu sakamakon Soshiyal Midiya mu na tallata jaruman mu kanana da bakin fuska wadanda ba a sa ni ba, kuma Alhamdulillahi duniya ta karba mun yi nasarar hakan, ba wai mu na kushe baya bane, amma dama rashin fadada abun ne ya sa wa su mutane a cikin mu ke nuna son zuciyar su, wannan shi ya janyo nakasun masana’antar fim a baya, amma yanzu da a ka kasa ta a faifai sai a ka gane cewar wadancan mutanen ba wai daga su bane ba, mutanen gari su na bukatar sababbin fuska da kuma sabon abu, wasu mutane ne kawai a kasuwa da kila son zuciyar su ko kuma kqila hadin baki ne tsakanin wadancan

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button