Sirrin Samun Daukakar Malam Isah Ibrahim Pantami
Daga: Datti Assalafy
Ba wani abu bane sirrin samun daukakar mutum a rayuwa sama da ya rabu da iyayensa lafiya suna masu sanya albarka da farin ciki a gareshi
Wannan da kuke gani a hoto na farko shine Mahaifin Malam Isah Ali Ibrahim Pantami, har zuwa ranar da zai koma ga Allah bai dena sanya albarka wa rayuwar Malam ba
Wadanda suke kansa a ranar da zai rasu, sunce magana ta kusan karshe da yayi a rayuwarsa na duniya kafin ya furta kalmar shahada a zare ransa shine: “Allah Ka yiwa Malam Isah albarka”, yayi ta maimaitawa kafin sai ya furta kalmar shahada ya rasu
Hakanan Mahaifyar Malam itama, ta kasance mai yawan sanya albarka wa Malam har zuwa lokacin da Allah Ya mata rasuwa, zaku ga a duk lokacin da Malam ya tuna da iyayensa ko ya tuna da falalar iyaye yana yawan yin kuka, yace babu addu’ah da tafi shiga ransa sama da wani yace Malam Allah Ya jikan iyayenka, saboda yadda ya shaku da su
Sannan ku dena ganin Allah Ya rufawa Malam asiri ya samu daukaka kuna masa hassada, ba’a banza ya samu ba, yasha wahala a rayuwa, yayi gwagwarmaya, Malam har kauyukan Gombe yake zuwa ya saro shinkafa ya kawo cikin Gombe ya siyar, yayi sana’ar sayar da gwanjo, yayi sana’ar dinki da gyaran babur da gyaran Computer
A haka Malam yayi ta tashi fadi wajen neman ilmin addini da na boko wanda sai da ya kai matakin digiri na uku, ya zama Farfesan ilmi a jami’ar Musulunci dake garin Manzon Allah (SAW) Madinah, daga karshe Allah Ya masa baiwa ya rabu da iyayensa lafiya suna masu amintuwa da farin ciki dashi da sanya albarka a gareshi
Wallahi wahalar da Malam yasha a farkon rayuwarsa da kuma biyayya da ya yiwa iyayensa da hidimar da ya yiwa addinin Musulunci shine Allah Ya ke saka masa a yanzu tun daga nan duniya, kuma ya dinga samun daukaka kenan har ya koma ga Allah
Don haka kai da kake yiwa Malam hassada inkai ba ‘dan tasha bane iyayenka suna raye je ka aikata abinda zasu sanya maka albarka, wallahi sai ka ga daukaka a rayuwa, kuma sai Allah Ya kareka kuma sai ka samu nasara akan komai har da makiya
Allah Ka gafartawa iyayen Malam da dukkan ‘yan uwa Musulmi da suka rasu, Allah Ka kare Malam Isah Ali da mu, Ka kyautata karshen mu Amin