Labarai
Shugaban hukumar NDDC ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da bincikarsa
Advertisment
Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake tsaka da binciken almubazzaranci da ake zargin hukumarsa da yi.
Lamarin ya faru ne a yau Litinin yayin da Daniel Pondei yake bayar da bayani ga ‘Yan Kwamitin Majalisar Tarayya kan yadda hukumar ta kashe biliyoyin naira.
A ƙarshe sai fitar da shugaban daga cikin ɗakin taron aka yi.
Bisa wannan dalili ne shugaban kwamitin ya bayar da sanarwar tafiya hutun minti 30, inda za su ci gaba da ƙarfe 1:35, a cewarsa.
A ranar Alhamis Mista Pondei ya fice daga zauren binciken ba tare da an kammala ba, sannan ya zargi shugaban kwamitin, Olubunmi Tunji-Ojo da cin hanci.
Bbchausa na ruwaito.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com