Kannywood
Shekara 12: Auren mu mutu-ka-raba, inji Muhibbat da Hassan Giggs
Advertisment
SHEKARA goma sha biyu a aure ba wasa ba ne. Duk zaman auren da ya shafe waɗannan shekarun, ka tabbatar da cewa ya ratso ruƙuƙin daji, ya tsallako kogi mai mahaukatan raƙuman ruwa, ya jure ruwa da iska da cida, ya biyo hanya mai gargada kafin ya shigo gari inda ma’auratan za su huta, su sakata su wala, su more daɗin soyayyar su da fahimtar junan su.
Hakan ne ya faru ga Hassan Giggs da Muhibbat Abdulsalam. Yau shekara 12 tun da daraktan ya auro fitacciyar jarumar daga Kaduna, ya kawo ta Kano a matsayin matar sa. Sun yi zama na soyayya da tallafar juna.
Auren babban darakta Giggs da Muhibbat – wadda ita ma kan ta darakta ce – ya na daga cikin aurarrakin ‘yan fim ɗin Hausa da ake kafa misali da su ta fuskar daɗewa da kuma zaman lafiya da ƙaruwar arziki a tsakanin ma’auratan. Har ta kai waɗannan ma’aurata biyu su na alfahari da cewar a duk tsawon waɗannan shekarun da su ka shafe ko sau ɗaya Muhibbat ba ta taɓa yin yaji ba.
A ranar 28 ga Yuni, 2020 ne dai auren nasu ya cika shekara 12. Hakan ya zamo abin alfahari ba ma a gare su kaɗai ba har ma da duk wani mai yi wa masana’antar finafinai ta Kannywood fatan alheri. Daga ranar, tun da Giggs ya bayyana a soshiyal midiya cewa auren nasu ya cimma wannan zangon, ɗimbin masoyan su sun taya su murna tare da yi masu fatan alheri.
Domin jin yadda rayuwar auren nasu ta kasance, wakilin mujallar Fim, MUKHTAR YAKUBU, ya zauna da Hassan da Muhibbat a gidan su a Kano don jin yadda su ka gudanar da al’amuran zaman auren nasu. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:
FIM: Ya ka ke ji auren ku ya cika shekara goma sha biyu a yau?
HASSAN GIGGS: Ka san komai nufi ne na Ubangiji, kuma da man an ce tun ran gini ran zane, kuma shi zaman aure idan ka samu mace wacce ta fito daga gidan tarbiyya, to ka ga ba ka da matsala kenan. Don haka iyayen ta sun ɗauke ni tamkar ɗan su na cikin su. Don haka ni dai babu abin da zan ce da Allah sai godiya. Mun zauna lafiya da iyayen ta, kamar yadda mu ke tare da Muhibbat Abdulsalam har yanzu ko yaji ba ta taɓa yi ba, don haka abin alfahari ne a gare ni da mu ka fahimci juna ni da ita. Don haka babu abin da zan ce da Allah sai godiya, domin a yanzu Allah ya azurta mu da haihuwar ‘ya’ya guda uku: farko mu na da Aisha, sai Fatima da Khadija. Allah mu na ƙara gode maka.
FIM: A matsayin saurayi da budurwa ku ka yi aure. Yanzu kun zama iyaye. Ko yaya Hassan Giggs ya ke ji a matsayin uba?
GIGGS: To, ni dai babu abin da zan ce, domin idan ka na so ka samar da yara nagari to ka fara da iyaye. To da yake da man ita Muhibbat kowa ya riga ya san ta a masana’antar finafinai mu ka haɗu da ita, kuma Allah ya haɗa mu mu ka yi aure kuma ga shi har Allah ya ba mu yara, don haka ina godiya ga Allah, ni dai ‘ya’ya na sun samu tarbiyya, saboda na yi sa’ar samar musu uwa tagari.
FIM: A naki ɓangaren, ko yaya za ki kwatanta shekaru 12 da ku ka yi a matsayin miji da mata?
MUHIBBAT ABDULSALAM: To, alhamdu lillah, Allah shi ne abin godiya, domin ni a yanzu ma ji na ke yi ina matsayin amarya, kamar yanzu na shigo gidan auren! Kawai dai ina kallon ‘ya’ya wanda shi ne ya ke tuna mini na ƙara girma da shekaru, don saboda Humaira ta kusan kamo ni a tsayi. To dai ina ƙara godiya ga Allah, saboda ba zan manta ba a lokacin da za a yi auren nan wasu na cewa da wuya idan za mu yi wata biyu ko uku, don haka sai aka rinƙa lissafi ana ƙirgawa, amma da ya ke abin na Allah ne sai ga shi a yau mun kai shekaru goma sha biyu, wanda kuma ina fatan mutuwa ce kawai za ta raba mu. Don haka tsakani na da miji na daga gidan sa sai makara zuwa maƙabarta in Allah ya yarda, don ba na fatan na rabu da shi na auri wani. In ka ji mace ta na yin wannan tunanin, to ba ta ji daɗin zaman auren ta ba ne. To mu alhamdu lillah, daidai gwargwado ina jin daɗi na, kuma kowa ya gan ni ya san akwai jin daɗi a gare ni da kwanciyar hankali.
FIM: Abin da ake ta faɗa shi ne ‘yan fim ba sa
zaman aure, amma ga shi ke da mijin ki har kun shafe shekaru ku na zaman ku lafiya.
zaman aure, amma ga shi ke da mijin ki har kun shafe shekaru ku na zaman ku lafiya.
MUHIBBAT: To gaskiya zan iya cewa Allah shi ya ƙaddara mana hakan, kuma zancen a ce ‘yan fim ba sa zaman aure, wannan ba gaskiya ba ne. Yadda auren ‘yan waje ya ke mutuwa ma, to na ‘yan fim ba ya mutuwa haka. Abin da ya sa ake sanin na ‘yan fim (shi ne) saboda su fitattu ne, don haka duk abin da ya faru a gare su ake ji, amma wallahi yanzu idan ka duba sai ka ga kusan zaurawa sun fi ‘yanmata yawa. Mu dai addu’ar da mu ke yi, Allah ka zaunar da duk waɗanda su ka yi aure a gidajen mazajen su, amma gaskiya ‘yan fim su na zaman aure.
FIM: To a matsayin ki na uwa mai tarbiyyantar da yara, ko yaya zamantakewar ki ta ke da maigidan ki da yaran ki?
MUHIBBAT: To, kamar yadda ya faɗa maka a baya, idan za ka yi aure ka nema wa yaran ka uwa tagari. To ba alfahari ba, ilimi daidai gwargwado na addini ina da shi, kuma da man an ce “Al ilmu kal miski,” wato ilimi kamar almiski ne – ko ka ɓoye sai ya bayyana. To babban ƙoƙarin da na yi, kamar Humaira ita ce babba, kuma tun ta na ƙarama na ke ta ƙoƙarin cusa mata wani abu a ƙwaƙwalwar ta, wanda na san cewar idan ta ɗauka, to rayuwar ƙannen ta ma za ta inganta.
Ka san shi matakin tarbiyya guda uku ne: 7 na farko, 7 na biyu, 7 na uku. Na farko ka yi wasa da su. Na biyu, ka sanar da su Ubangijin su da Manzon Allah, kuma ka koyar da su Alƙur’ani da sauran abubuwa na addini. Don haka idan ɗan farin ka ya samu, to da yardar Allah sauran za su samu. Domin a yanzu ko ba na nan, a yadda na ke tsara musu karatu, to Humaira za ta zaunar da su su yi muraja’a, don haka har bulala na saya mata don ta ke kula da su ta yi musu kari ta kuma tabbatar sun yi tilawar na baya. Haka mu ke yi. Kuma su na zuwa Islamiyya, su na zuwa boko. Duk da ina harkokin kasuwanci na, da ya ke na tsara abin, ba na samun matsala.
GIGGS: To Hassan Giggs, a matsayin ka na maigida da nauyin komai ya ke a kan ka, ko wanne irin darasi ka samu na ɗaukar ɗawainiyar gida a tsawon zaman ku?
GIGGS: To da man na faɗa maka, kuma zan ƙara maimaita maka, tun ran gini ran zane. Mu da man auren mu ba mu ɗora shi a kan ƙarya ba, wanda za a zo ana samun matsaloli. Don haka mu na taimaka wa junan mu, mu na rufa wa juna asiri, domin a kan samu wasu lokutan ko tafiya na yi kafin na dawo ta shirya wasu abubuwan, sai dai ta sanar da ni abin da ta yi ta ce, “Idan Allah ya hore maka sai ka biya daga baya.” To irin wannan zaman mu ke yi, don ba mu ɗora auren mu a kan ƙarya ba kamar yadda wasu su ke yi, sai daga baya kuma su zo su yi ta samun matsala. Don haka mun gina auren mu ne bisa soyayya tsakani da Allah, shi ya sa ni ɗaukar nauyin iyali na ba ya yi mini wahala; daidai gwargwado ina iya ƙoƙari na, kuma alhamdu lillahi.


FIM: Ta ɓangaren zaman auren ku da matar ka, ana yi maku kallon kamar zama ne na mata, ‘yar’uwa, abokiyar aiki.
GIGGS: To ai da man tun da aka yi aure, an riga an zama ‘yan’uwan juna, duk da cewar yanayin aikin mu iri ɗaya ne, don a harkar fim mu ka haɗu da juna har Allah ya ƙaddara ita mata ta ce ni mijin ta ne, kuma har yanzu mu na cikin masana’antar tare.
FIM: Muhibbat, a matsayin ki na uwargida, yaya ki ke kallon maigidan ki wajen zamantakewar auren ku?
MUHIBBAT: To, na farko ina kallon sa a matsayin miji na, sai kuma kallon sa da na ke yi a matsayin babban aboki na, sai kuma kallon sa da na ke yi a matsayin oga na a harkar fim, saboda ka san ni ma darakta ce kuma shi ne ya koya mini, sannan kuma abokin gulma na ne, wanda ba zan ɓoye masa komai ba, don haka abokin sirri na ne, don na san ba zai taɓa fita waje ya tona mini asiri ba. Sannan a wajen kasuwanci na na magungunan mata za ka ga cewar nawa ya fita daban saboda taimakon da ya ke ba ni, don haka abokin arziki na ne, kuma uban ‘ya’ya na, kuma wanda na ke sa ran har a Aljanna ma mu na tare. Babban abin baƙin ciki na dai da ba za a bar ni daga ni sai shi ba, sai an haɗa mu da Hurul’aini!
FIM: Daga zaman auren da ku ka yi na tsawon shekaru, ko wanne darasi masu niyyar aure da masu auren ma za su samu daga gare ki?
MUHIBBAT: To abin da zai zamo darasi shi ne, na farko, su gina auren nasu a kan gaskiya. Sannan na biyu sai mace ta daure ta zama mai haƙuri, domin wani lokaci za ka ga kai-tsaye ba wai mijin ki ne zai ɓata miki rai ba, ba mamaki dangin sa ne, ko maƙoci ko kuma a karan kan sa. To fa idan babu haƙuri da juriya, to zai iya shafar zaman auren saboda ita ƙwaƙwalwa ba ta son abin da zai rinƙa taɓa ta, don haka idan ba ki yi haƙuri ba to da wuya ki iya zaman auren. Don haka ma’aurata a riƙa haƙuri, juriya da kuma gaskiya, sannan a dage da addu’a a kowanne lokaci.
FIM: Kai kuma wacce shawara za ka bayar?
GIGGS: To, matasa dai shawarar da zan ba su shi ne su riƙe gaskiya da amana, kada su yi wa yarinya ƙarya daga ƙarshe abin ya zo ya zama matsala. Domin aure na da Muhibbat aure ne na sauƙi da jin daɗi wanda na samu daga wajen iyayen ta, don haka duk wani kuɗi da na shirya zan kashe a auren a wasu bidi’o’i sai mahaifin ta ya hana ni, ya ce na ajiye kuɗin domin akwai yanayi da ake shiga bayan an yi aure, don haka sai na yi amfani da kuɗin a lokacin. To ka ga an samu iyaye nagari, dattijai. Don haka auren ya zo da sauƙi, kuma mu ke ganin sauƙin har yanzu.
Don haka matasa su san ‘yar wanda za su auro ta zama abokiyar zaman su. Don haka duk abin da za su yi, su yi shi bisa kyakyawar niyya.
FIM: To ba don ka na kusa da ita ba da sai na ce ko ka na da niyyar ƙara aure?
GIGGS (dariya): To ni idan ma zan yi aure to ba zan yi adalci ba, don haka a yanzu ba ni da niyyar ƙara aure.
FIM: Muhibbat, da alama dai kin rufe ƙofa, don ga shi mijin ki ya ce ba zai ƙara aure ba.
MUHIBBAT: To ni ban hana shi ba; in dai akwai wadda ya ke so, ina shirye da na zauna da ita, domin da a ce miji na ya je ya na bin mata a waje gara ya ƙaro aure. Amma tunda ya ga na ishe shi, to shi kenan. Amma in zai iya adalci, ya ƙaro, don ba zan so ranar kiyama ya tashi da rabin jiki a shanye ba! (dariya)
Daga ƙarshe, Hassan da Muhibbat sun yi wa jama’a masu taya su murnar cika shekara 12 da auren su godiya tare da fatan alheri.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com