Addini
Sautin Murya : Hukuncin Laifin Fyade Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano
Ga Yadda hukuncin yake – Daga Daurawa :-
Ana duba idan ya yi amfani da makami ko karfi, Saboda haka wanda ya yi wa mace fyade ta hanyar amfani da makami hukuncinsu guda da wanda ya yi fashi da makami, ma’ana hukucinsa kisa kai tsaye
Idan ya kasance mace ce mai girma kuma akwai laifinta a wannan bangaren to hukuncin zina ne ya hau kan wanda ya yi fyaden, hukuncin zina kuwa dama idan yana da aure to za a kashe shi, idan kuma bai taba aure ba to za a yi masa bulala 100 da daurin shekara guda da kuma tarar dala dubu 80 (kwatankwacin Naira miliyan 31) kamar yadda aka kayyade a yanzu.
Idan karamar yarinya aka yi wa fyade, malamai sun yi fatawar cewa hukuncinsa na kisa ne, idan kuma diyya za a karba to kwatankwacin ta kisa za a karba, domin kuwa ya lalata ta, idan kuwa dama mutum ya lalata wa mace mutuncinta ko ita ta lalatawa namiji to diyyarsa daidai take da ta rai – wanda a yanzu aka kiyasta akan naira miliyan 66 ko rakumi 100 ko Saniya 200 ko rago 2,000 ko dirhami 12,000
Idan kuma namiji aka yi wa fyade to hukuncin kisa ne saboda kai tsaye ya zama luwadi wanda kuma aka yi wa za a kare masa mutuncinsa da biya masa kudin kare lafiyarsa.
Idan kuwa karamar yarinya ce ko da ba a yi amfani da makami ba hukuncin na kisa ne.
Idan mace da amincewarta ta je inda ta san za a yi mata fyade to ita ma za a mata hukunci.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com