Labarai

Sarkin Burunei, Sarki Mai Motocin Alfarma Fiye Da 7,000 (Hotuna)

Advertisment

Sarki kuma Firayi Ministan Burunei dake Asiya, Hassanal Bolkiah, ya zama ɗaya daga cikin sarakuna mafiya dukiya kuma mafiya faɗa a ji a wannan ƙarni na 21.

Sarki Bolkiah yana rayuwa ta ƙawa da tarin motocin alfarma da fada ita ma ta alfarma.

Sarkin ya fara shirya yin rayuwa ta ƙawa tun lokacin da aka haife shi ranar 15 ga Yuli, 1946 a Istana Darussalam, dake garin Brunei.

Ɗauki sunansa alal misali, ana ce masa Hassanal Bolkiah, amma cikakken sunansa shi ne: Kebawah Duli Yang Maha Mulia Paduka Seri Baginda Sultan Haji Hassanal Bolkiah Mu’izzaddin Waddaulah ibni Al-Marhum Sultan Haji Omar ‘Ali Saifuddien Sa’adul Khairi Waddien, Sultan dan Yang Di-Pertuan Negara Brunei Darussalam, kamar yadda jaridar GhGossip ta rawaito.

Mujallar Forbes dake New Jersey City a Amurka ta sa Sarki Bolkiah a jerin mutane mafiya arziƙi a duniya, domin kuwa an ƙiyasta cewa tarin dukiyarsa ya kai dalar Amurka biliyan $20 a 2008.

Sarki Bolkiah shi ne sarki na biyu mai ci mafi daɗewa a kai mulki banda Sarauniya Elizabeth II.

Sarki Bolkiah ya yi bikin cikar sa shekara 50 a kan mulki shekaru uku da suka gabata.

A cewar wani rahoto da Carmudi ta fitar, Sarkin na Burunei yana son motoci masu tsada, kuma a kodayaushe yakan son ya siyi mota mafi sabunta.

Rahotonni sun bayyana cewa Sarkin yana da mota ƙirar Ferrari 456 GTs guda 70, ƙirar Bentley Turbo Rs guda 80, ƙirar BMW 750iLs guda 25.

A cewar rahotonn, Sarki Bolkiah nada ƙananan motoci fiye da 7,000 da suka haɗa da:

Rolls Royce – guda 604
Mercedes-Benz – guda 574
Ferrari – guda 452
Bentley – guda 382
BMW – guda 209
Jaguar – guda 179
Koenigsegg – guda 134
Lamborghini – guda 21
Aston Martin – guda 11.

Duk da haka, akwai motoci na kece raini da aka tanada don su yi daidai da rayuwar Sarki Bolkiah ta alfarma. Waɗannan motoci sun haɗa da:

Rolls-Royce Phantom VI
Mercedes-Benz CLK GTR
24-Carat Gold-Plated Rolls Royce
Bentley Java
Ferrari Mythos
Ferrari FX
Rolls Royce Phantom II Continental – Star of India
Aston Martin V8 Vantage Special Series II
McLaren F1
Mercedes-Benz S73 T AMG wagon

Kadan daga cikin hotunan motocin sa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button