Labarai
Riga-kafin Coronavirus: binciken Jami’ar Oxford ya yi nasara
Advertisment
Riga-kafin cutar korona da aka samar a Jami’ar Oxford da alama ba shi da matsala kuma yana bijiro da garkuwar jiki.
Gwajin da aka yi wa mutum 1,077 ya nuna cewa allurar tana sanya wa jiki ya fito da garkuwar da kuma kwayoyin halitta da za su iya yakar cutar korona.
Binciken yana da gagarumar alamar yin nasara, amma ya yi wuri a san cewa hakan ya wadatar wajen ba da kariya, kuma za a yi gwaji mai girma nan gaba.
Tuni Burtaniya ta bukaci sayen riga-kafi miliyan 100.
Ta yaya riga-kafin yake aiki?
Ana ci gaba da samar da riga-kafin mai suna ChAdOx1 nCoV-19 cikin wani irin sauri mai ban mamaki.
An samar da shi ne daga wata kwayar cuta da aka ƙirƙiro wacce take jawo mura ga birrai.
An inganta ta sosai tun farko, ta yadda ba za ta iya haifar da cuta ga mutane ba kuma za ta yi kama da cutar korona.
Masana kimiyya sun yi hakan ne ta hanyar mayar da bayanan kwayoyin halittar da cutar korona take bunkasa da su – wanda suke taka rawa wajen ratsawa cikin kwayoyin halitta – a kan riga-kafin da suke samarwa.
Hakan na nufin riga-kafin ya yi kama da cutar korona kuma tsarin kare garkuwar jiki zai iya yakarsa.
Ana amfani da samfurin mutane wajen gwada riga-kafin
Ba shi da illa?
Eh, amma akwai illoli kadan.
Babu wata mummunar illa idan an yi riga-kafin, sai dai kashi 70 cikin 100 na mutane su kan dan yi fama da ciwon kai ko masassara.
Masu bincike sun ce za a iya magance hakan da kwayar paracetamol.
Farfesa Sarah Gilbert ta Jami’ar Oxford A Burtaniya ta ce: “Har yanzu akwai sauran aiki kafin mu tabbatar da cewa ko riga-kafin zai taimaka wajen shawo kan annobar cutar korona, amma wadannan sakamakon na farko sun sa muna da kyakkyawan fata.”
Wadanne matakai ne na gaba a gwajin?
Zuwa yanzu dai sakamakon ya nuna akwai kyakkyawan fata, amma babban abin da ake bukata daga riga-kafin shi ne ya kasance mara illar da za a iya bai wa mutane.
Binciken ba zai iya nuna ko riga-kafin zai iya kare mutane daga rashin lafiya ba ko kuma ya rage alamun da suke nunawa na Covid-19.
Fiye da mutum 10,000 ne za a yi wa gwajin a matakin farko a Burtaniya.
Haka kuma an fadada gwajin zuwa wasu kasashen saboda cutar korona ta yi ƙasa a Burtaniya, abin da ya sa za a sha wuya wajen gane ko riga-kafin yana aiki.
Za a yi babban gwaji da zai hada da mutum 30,000 a Amurka da 2,000 a Afirka Ta Kudu da kuma 5,000 a Brazil.
Zan samu a yi min gwaji?
Akwai yiwuwar samar da riga-kafin zuwa karshen shekarar nan, amma ba zai samu a ko ina da ina ba.
Ma’aikatan lafiya za a bai wa fifiko da kuma wadanda suka fi fuskanta barazanar kamuwa da cutar korona saboda yawan shekarunsu.
Haka kuma, samuwar riga-kafin da wuri watakila sai badi idan komai ya tafi daidai.
Wane ci gaba aka samu a samar da riga-kafin?
Riga-kafin na Oxford ba shi ne na farko da ya kai wannan mataki ba, akwai wasu kungiyoyin a Amurka da China ma da suke wannan aikin.
A jumulla akwai riga-kafin cutar korona 23 da ake kan gwada su a fadin duniya da kuma wasu 140 din da suke matakin farko-farko na gwaji.bbchausa na ruwaito.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com