Rashin banbanta kasuwancin mu da harkar fim ya sa sana’ar mu ba ta zuwa ko ina – Sapna Maru
Kusan duk wata’ yar fim da za ka ga ta na harkar kasuwancin ta ba ya wuce kayan kwalliya wadanda su ka hadar da Atamfa Yaduka da Shaddodi, sai kuma kayan shafe-shafe da wajen gyaran jiki, sai wa su kadan da su ke bude wajen sayar da abinci.
Jarumai da yawa a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood su na da wannan tsarin kasuwancin in da su ke bude manyan kantuna. Daga cikin su akwai Sapna Aliyu Maru, Fati Baffa Fagge, Maryam Yahaya, Aina’u Ade, Mansurah Isah, Ali Nuhu, Isah A Isah, Nura Hussaini, Sani Musa Danja, Sai kuma wadanda karfin su bai kai na su bude kantuna ba, sai dai su rinka tallan kayan a shafukan su na sada zumunta. Su ma wadanda su ka shahara a fagen wannan kasuwancin a shafukan su na kafar sada zumunci sun hada da Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a, Maimuna Muhammad, Teemah Makamashi, Muhibbat Abdussalam, Halisa Muhammad da sauran su. Ma su bude wajen sayar da abinci kuwa akwai tsohuwar jaruma, Maryam Abubakar Jankunne, ko da yake a yanzu ita kadai ce ta rage cikin wadanda su ka bude wajen sayar da abinci sauran duk sun rufe. T
Amma me ya sa ‘yan fim ba sa yin wani kasuwancin sai na sayar da kayan kwalliya?
Wannan ita ce tambayar da mu ka yi wa wa su daga cikin jaruman. Hauwa S Garba ta na cikin jaruman da mu ka yi wa tambaya dangane da kasuwancin na’ yan fim wanda ya takaita ga kayan kwalliya, inda ta amsa mana da cewar.
“To ka san su ‘yan fim su a karan kan su kwalliya ne, domin haka kasuwancin kayan kwalliya zai fi dacewa da su. Yanzu idan ka kula a duk duniya duk wani kayan kwalliya da’ yan fim da mawaka a ke tallata su, domin haka al’adar ‘yan fim da mawaka ne tallan kayan kwalliya, saboda da alakar su da kayan. Kuma yanzu idan a ka ce wata jaruma ta bude wajen sayar da kayan kwalliya ko gyaran jiki to sai ka ga an fi zuwa wajen, saboda a gan su ma, to ka ga wannan sana’ar ta fi dacewa da’ yan fim”.
Ita kuwa Sapna Aliyu Maru, cewa ta yi”Gaskiya mu ‘yan fim wannan kasuwancin ina ganin shi ne ya fi dacewa da mu, domin ni ka ga ina fita waje sayen kaya, kamar Dubai, India da sauran kasashe, to duk in da muka je harkar mu ta fim tana Kara mana martaba a wajen abokan kasuwancin mu musamman wadanda mu ke tafiya tare da su. Amma dai abu da ya ke da muhimanci shi ne mu rinka bambanta kasuwancin mu da harkar fim a wajen gudanar da kasuwancin, rashin bamabantawar ya sa wa su ko da sun fara kasuwancin na su ba ya zuwa ko’ina”. Inji Sapna
SHAGALIN BIKIN BIRTHDAY NA MARYAM YAHAYA (FULL VIDEO)
??????????
https://youtu.be/YutL6cllSng