Labarai

Masu cin moriyar shirin N-Power 14,020 Ba za su Samu Alawus ba ~ Sadiya Farouk

Advertisment

Ma’aikatar kula da ayyukan jin kai, bala’o’i da ci gaban al’umma, ta sanar da cewa, akwai masu cin moriyar shirin N-Power 14,020 masu karbar albashi a wasu ma’aikatu na gwamnati daban-daban.

Shirin N-Power wanda aka kirkiro tun a shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta samar da shi domin daukar matasa marasa aiki da suka kammala karatu, kuma aka sanya musu alawus na N30,000 duk wata.

Cikin wata sanarwa ta ranar Alhamis da Rhoda Iliya, mataimakiyar darekatan labarai ta ma’aikatar ta fitar, ta ce ba za a biya wasu masu amfanar shirin N-Power alawus ba saboda an gano suna karbar albashi a wasu ma’aikatun na gwamnati.

Ta ce ofishin Akanta Janar na kasa na kokarin ganin an warware matsalar biyan bashin alawus din watannin baya ga masu cin moriyar shirin na N-Power da suka cancanta.

Advertisment

Ministar kula da ayyukan jin kai, bala’o’i da ci gaban al’umma; Sadiya Umar Farouq
Don haka Ministar kula da ayyukan jin kai, bala’o’i da ci gaban al’umma, Sadiya Umar Farouq, ta ke ba da hakuri a kan jinkirin da tantance masu cin moryar shirin N-Power na hakika ya haddasa.

Ta ce babu shakka da zarar ofishin Akanta Janar na kasa ya kammala warware matsalar, za a saki alawus din ga wadanda suka cancanta.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a baya bayan nan ne ma’aikatar kula da ayyukan jin kai, bala’o’i da ci gaban al’umma, ta bayyana cewa za’a sallami matasan N-Power da aka dauka a shekarar 2016 a watan Yuni, 2020.

Hakazalika za’a sallami wadanda aka dauka a 2018 a watan Yuli, 2020. Shirin N-Power ya dauki matasa 500,000; karon farko an debi mutane 200,000 a Satumban 2016, sannan 300,000 a watan Agustan 2018.

A lokacin da aka daukesu aiki, an bayyana musu cewa watanni 24 za suyi amma matasa 200,000 farko da aka dauka sun kwashe sama da watanni 40.

Matasan sun ce basu ki a sallamesu ba, amma a biyasu kudin albashin watanni biyu da ba’a biyasu ba har yanzu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button