Labarai
Masha Allah :Shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan Ya jagoranci sallar Juma’a a Hagia Sophia Cocin Da Ya Mayar Masallaci (Hotuna)
Advertisment
Shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan ya jagoranci sallar Juma’a a cikin shahararren ginin nan mai dimbin tarihi na Hagia Sophia wanda ya shafe daruruwan shekaru a matsayin Coci kafin a mayar da shi Masallaci.
Al’ummar Musulmi masu tarin yawa ne suka halarci sallar Juma’ar na yau duk da sharuddan nesa nesa da juna da dokar sanya kyallen rufe baki da hanci da aka kafa domin hana bazuwar cutar coronavirus.
Shugaba Erdogan ya halarci sallar ce tare da ministocinsa.
Tun da farko dai, an samar da wannan kasaitaccen gini ne a matsayin Coci a Daular Gabashin Roma, sai dai kuma daga bisani aka mayar da shi Masallaci, wato bayan Daular Usmaniya ta ci birnin Santanbul a shekarar 1453.
A shekara ta 1935 ne mutumin da ya assasa Turkiya wadda babu ruwanta da addini, Kamal Ataturk , ya mayar da ginin a matsayin wajen adana kayan tarihi.
Ko a yau Juma’a sai da kasar Girka ta soki matakin mayar da ginin Masallaci, yayin da wasu kungiyoyin Kiristoci ka cewa, wannan rana ta zame musu ranar zaman makoki saboda mayar da ginin Cocin Masallaci.
Advertisment
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com