Kannywood
Kada a saka mawaƙa a aikin tace waƙoƙin yabon Manzo, inji Mahmud Nagudu
Advertisment
FITACCEN mawaƙin nan na Kannywood, Mahmud Nagudu, ya yi kira ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da kada ta kuskura ta saka mawaƙan yabon Manzon Allah (s.a.w.) a cikin kwamitin tantance waƙoƙin yabon da za ta kafa. Fim magazine ruwaito
Nagudu, wanda shi ma ƙwararre ne a fagen waƙoƙin yabon Manzon Allah, ya faɗi haka ne a hirar sa da mujallar Fim.
A cewar sa, “Ina kira ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da kada ya kasance sun sa masu waƙar a cikin tace waƙoƙin da za a yi, don ya zamo tace waƙar ba masu waƙar ba ne.
“Saboda idan da akwai masu waƙar a ciki, za ka samu wani da aka saka shi a cikin kwamitin tacewar shi ma ya kamata a tace shi.
“Saboda haka kamata ya yi a kirawo wanda ba harkar sa ba ce, kuma ya zamo an samu bambancin fahimtar addini a cikin kwamitin, domin kuwa dukkan Musulmin duniya ya na da alaƙa da Manzon Allah, sai dai in mutum ba Musulmi ba ne.”
Idan kun tuna, kwanan nan ne hukumar ta bayyana cewa za ta fito da wani tsari na tantance mawaƙan yabon Manzon Allah da bada izini ga kowane mawaƙi da zai shirya majalisi a faɗin jihar.
Bayyana sabon tsarin ya haifar da ka-ce-na-ce, inda wasu ke cewa hakan ya dace, wasu kuma na cewa bai dace ba.
Ɗaya daga cikin manyan mawaƙan yabon Annabi, Malam Bashir Ɗandago, ya nemi hukumar da ta tabbatar da cewa ta saka mawaƙan yabon a kwamitin tantancewar.
A wata hira da ya yi da Fim kwanan nan, Malam Bashir ya bayyana cewa idan har malamai kaɗai aka saka a cikin aikin, to ba za su yi wa mawaƙan adalci ba domin kuwa akwai wata gasa daɗaɗɗiya a tsakanin su.
Shi ko a nasa ɓangaren, Nagudu cewa ya yi malamai kaɗai ne ya kamata su kasance ‘yan kwamitin.
Ya ce, “A kirawo malamai masu fasaha, masana waƙa da hikima da balaga da sanin ya ake yi a shigar da maganganu.
“Domin akwai abin da in na faɗa maka yabo ne, amma idan na faɗa wa Manzon Allah sai ya zama an aibata shi.”
A yayin da ya bayyana sabuwar dokar da cewa ta dace matuƙa, sai mawaƙin ya ƙara fa cewa, “Yabon Manzon Allah (s.a.w.) ba ƙaramin abu ba ne domin kuwa tun da aka yi duniya babu wani abu da aka yi da ya kai darajar Annabi Muhammadu, don haka ma yabon sa wani al’amari ne mai girma.
“Duk abin da zai kare mutunci da darajar sa, to shi ne abin kiyayewa. Ya fi uwa da uba a wajen mu.”
Mawaƙin ya ƙara da cewa, “Wannan doka da aka samar, ni a waje na, ta fi mani komai, don haka ya na da kyau a ce an tace waɗanda za su yi yabo, domin ya zama a san me za su faɗa.
“Ka san kullum mu na yin abu ne yawanci don a burge, kamar maganar da za ta yi nesa da kai a Wuta, domin mutum sai ya rinƙa faɗar kalma wadda bai ɗauke ta komai ba amma a wajen Allah kalmar ta na da girma, kuma wannan za ta iya janyo mutum ya yi nesa a cikin Wuta, har ya zama Allah ba zai yi masa afuwa ba.
“Don haka wannan tsarin na tace masu yabon Manzo abu ne mai kyau.”
Nagudu ya buƙaci hukumar da ta duba yadda za a yi a yi aikin tantancewar, “kamar a ce a bada wasu matakai da su ake bi wajen tace mawaƙan, kamar ka san kaza ka san kaza.”
Wata shawarar kuma, inji shi, ita ce gwamnati ta yi ƙoƙari ta shirya wa mawaƙa masu yabon Annabi taron horaswa, inda za a sa malamai su ganar da su yadda magabata su ka yi nasu waƙoƙin yabon, “tun daga kan Sahabbai har zuwa kan su Alfazazi da Imamul Busari.”
Nagudu ya yi kira ga mawaƙan yabon Manzon Allah da su mara wa hukumar baya kan wannan dokar. Ya ce: “Maganar adawar siyasa ko wani abu bai shafi wannan abin ba, domin kuwa Manzon Allah shi ne a gaba.”
Ya ƙara da cewa idan hukumar za ta kafa kwamitin tantancewar, to ta nemi waɗanda su ka dace, ta naɗa su.
“Kada a ɗebo waɗanda su ke yin waƙar, don ta yiwu wani ɗan Tijjaniyya ne a ɗauko ɗan Ƙadiriyya ya rinƙa ganin ba a yi masa adalci ba saboda ba ƙungiyar su ɗaya ba.
“Don haka a nemi masana a kan harkar nan da su ke jin tsoron Allah, su ke son Annabi da gaske.”
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com