Labarai

Jama’a Ku Ankara Da Wannan Makirci Da Kuma Damfara Akan Inksnation akwai Hotuna masu Muhimmanci a Ciki ~ Datti Assalafy

Akwai wani shiri INKSNATION da ya karade kasarnan mutanen birni da kauye suna ta bude Gmail address maza da mata har ma da jarirai ana karban kudi naira dubu daya (1000) ana cika musu tsarin na INKSNATION

Da zaran an cika shirin sai kaga an turo maka da kudi Naira miliyan biyu (N2,000,000) amma ta Gmail dinka, cewa sai ranar 12 ga watan 8 (August) za’a fara diban kudin, kuma kullun dubu hudu (4,000) kyauta, akan wani tsari wai shi GLOBAL FAMILY RESERVE don a yaki talauci a duniya, ya zama nan da watanni tara babu wani talaka a duniya.

To amma bincike gameda wannan tsarin na INKSNATION ya nuna cewa wannan tsarin makirci ne da kuma damfara tare da hadin gwiwa ‘yan raji kafa gwamnatin bai daya a duniya, karen farautarsu wani bamaguje ne mai suna Amos Sewanu Omotade makaryaci ‘dan damfara mai da’awar Annabta matsafi ‘dan kungiyar asiri me aiki da tunanin karfin kwakwalwa shine ya kawo wannan tsarin

Yace yayi mafarki wai Allah ne ya zo masa a siffar ruhi yace masa ya nadashi Annabta ko Khalifa a doron duniya, don haka yana so ya raba mutanen duniya da talauci su bar bautar kowa su koma bautar Allansa  don su hada wata babbar katafariyar dakin bautar Allansu, don haka hanyar da zasu raba mutane da talauci shine suka fito da wannan shiri na INKSNATION

Yanzu idon mutanen mu ya rufe, maza da mata manya da kananan yara Musulmai kowa cikawa yake ba tare da sun san abinda shirin ya kunsa ba, har da ATM card ake musu na ciran kudin, ba tare da sunsan cewa wannan tsarin na ‘yan damfara ne da kuma kafurai masu da’awar Annabta da hadin gwiwar ‘yan kungiyar asiri

Musulmai kuyi hankali da makircin makirai da kuma ‘yan damfara, imba haka ba za’a jefaku cikin sahun kafurci da bautar shaidanu ba tare da kun sani ba, talauci ai ba hauka bane

Ina da Littafi PDF wanda yake kunshe da bayanan sirrin INKSNATION da tarihinsu da kuma manufarsu wanda suka rubuta da harcen turanci, kamar yadda zaku ga nayi screenshot na wasu shafin Littafin, idan kuna bukata sai na tura Littafin ta Group WhatsApp da Telegram

A madadin Hausaloaded da zarar ya fitar da wannan littafi zamu kokari mu kawo muku shi.

Allah Ya sauwake.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button