Labarai

INNALILLAHI : Yanzu Yanzu Majalisar Dattawan Nigeria Ta Dakatar Da Shirin Buhari Na Daukan Matasa 774,000

Advertisment

Yanzu yanzu Majalisar Dattawan Nigeria ta dakatar da shirin Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari na daukan mutane dubu dari bakwai da saba’in da hudu aiki wanda a kowace karamar hukuma za’a dauki mutum dubu daya

Dalilin da ya sa Majalisar Dattawa ta dakatar da wannan shirin shine musayar kalamai da sukayi jiya tsakanin su da Ministan kwadago Barrister Festus Keyamo, inda suka bukaceshi da ya mika musu ragamar diban aikin shi kuma yaki amincewa, daga bisani suka masa koran wulakanci daga majalisar

Yanzu dai muna jiran martani daga fadar shugaban Kasa bisa dakatarwan da majalisar Dattawa tayi na diban ma’aikata da shugaba Buhari ke son yi

Anyi walkiya anga kowa, duk wani mai adalci yanzu ya kamata ya fahimci su waye suke mayar da hannun agogo baya, kuma suwaye suke kawo ma shugaba Buhari cikas a kokarinsa na tabbatar da adalci wa kowa

Gashi dai abin alheri ne wanda kowa zai mora, amma sun dakatar saboda ba’a basu damar da zasu kawo ‘yan jagaliyar siyasarsu ba, to wannan abinda ya bayyana kenan a bangaren diban ma’aikata da samarwa talakawa saukin rayuwa, saura babban wato bangaren tsaro

Ba komai, mu kam dama mun san shugaba Buhari mutumin kirki ne, mai son kwatanta gaskiya da adalci ne, niyyarsa mai kyau ne, sai dai Allah Ya jarrabeshi da wasu irin abokan aiki

Yaa Allah Ka taimaki shugaba Buhari, Allah Ka bashi nasara akan maciya amana da ‘yan jari hujja Amin.

Daga Datti Assalafy

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button