Imani A Zuci Yake ! Ba Komai Bane Dan Nayiwa Ɗan Wannan Aski ~ Ty Shaba
Wani sabon Salon aski da mawaki FreiiBoi ya yi a cikin sabuwar wakar Ayaraye Amarya, wadda T Y Shaba da Asiya Ahmad su ka fito a matsayin Ango da amarya ya tayar da kura tare da daukar hankalin ma su kallo. Sai dai duk da cewa dai a yanzu ne a ke aikin wakar, domin haka wani bangare ne na wakar ya bayyana, amma dai mutane na kalubalantar salon wakar.
Kasancewar T Y Shaba a matsayin Uba ga shi FreiiBoi Shaba, kuma duk a na dora alhakin yin wannan Salo na askin a gare shi, hakan ne ya sanya mu ka ji ta bakin sa kan lamarin wanda ya fara bayyana mana cewar.
“Shi asalin wakar ma dai tun da farko, dana FreiiBoi shi ne ya shirya wakar, to amma ganin yadda ta karbu, musamman ma dai a wajen mata,’yan mata da wadanda su ke gidajen auren su, to wakar ta ja hankali, shi ya sa mu ka tsaya mu ka yi mata aiki sosai, wanda a cikin wannan aikin wakar ta hada mutane da yawa, kamar ni na fito a matsayin Angon sannan Asiya Ahmad kanwar Samira ta fito a matsayin Amarya. Sannan akwai mutane da mu ka gayyata daga jihohin kasar nan irin su Kabilu Kala da dai sauran su, mun kuma tsara sun zo taya ni bikin auren mu da Asiya, sannan shi kuma FreiiBoi ya zo a matsayin mawakan da zai wake Ango da Amarya a wajen wannan taron biki”.
Kamar mu al’adar mu ta Hausa idan ka kalli wakar za ka ga ta yi hannun riga da zubin al’adun mu na Arewa ko ya wannan batun ya ke?
“To zan iya ce maka alakar wakar da al’adar Bahaushe, shi ne wajen shirya wakar, domin za ka ga wajen da a ka shirya wakar za ka ga yanayi ne na masarautar kasar Hausa, domin haka duk wanda ya kalli wakar ya san al’adar kasar Hausa ce da Fulani to ka ga wajen da a ka yi wakar da lafazin da a ka yi wakar ya isa ya nuna maka al’adar kasar Hausa. Amma dai abun da za ka lura shi ne, mu a matsayin mu na ma su kawo wa matune abun da ya dace mu na kokarin yada al’adun mu a duniya, mu ba ma zancen bangaranci a ciki. Mu so mu ke Nijeriya ta zo a matsayin tsintsiya madaurin ki daya, domin haka a wannan tsarin idan za ka yi babu ruwan ka da cewar Igbo ko Yoroba da sauran su, saboda haka ne ma mu ka yi kokarin hada kabilun Nijeriya a cikin wakar, saboda ya zama Bahaushe dan uwan kowanne yare ne a Nijeriya”.
Abun da ya fi Jan hankali shi ne Askin da danka ya yi kuma ya fito a matsayin mawaki a wajen bikin b aka gani ya haifar da ce-ce-kuce tun da an ce inda baki ya karkata ta nan yawu ke zuba?
“A to da farko dai ina so a gane cewar shi FreiiBoi wakar Hip Hop ya ke yi, to kuma shi irin wannan askin da ya ke kan sa ya na daga cikin al’adar ‘yan Hip Hop, kuma a wakar ba wai mu na kallon FreiiBoi a matsayin Bahaushe ba ne, ya fito ne a matsayin Dan Nijerya da ya ke wakiltar kowanne bangare na kasar. Kuma a matsayin tsari na waka kowane Darakta ya na fitar mata da tsarin ta a yi yadda ya ke so wakar ta zo a aika ce ba a al’adance ba, to wannan tsarin da ya zo, za ka ga wani irin dinki ne ya saka shigen na Atamfa, sannan Gilashin da ya sa za ka ga duk wani mawakin Hip Hop a Nijeriya za ka ga irin wannan Gilashin ya ke sakawa askin sa kamar Salo da tsari ne na Hip Hop, domin haka abun da tsarin ya zo kenan, abun da zai ba ka mamaki a ranar da za a yi aikin a ka yi askin da a ka gama aikin wakar kuma a ranar aka aske shi, domin haka an yi askin ne saboda wakar kuma da a ka gama a ka aske ka ga babu wani abun tambaya a ciki”.
A matsayin ka na Uba ko me ka ke fatan dan ka ya zama nan gaba?
“E to ba ni ne na ke da zabin ya zama wani abu ba, domin kuwa irin wannan matsalar mu ke samu musamman a Arewa, za ka ga Uba ya tashi ya na hira da abokan sa ya na cewa ni Dana so na ke ya zama abu kaza, amma ba ya tunanin dan sa ya na da kwakwalwar da zai zama haka din. Sakamakon haka ni abun da Dana ya fi kwarewa shi zan ba shi kwarin gwiwa ya yi kamar yanzu ya na da sha’awar ya zama direban jirgin sama, domin haka sai na saka shi a tsarin karatun da zai kai ga cimma burin sa, kuma haka iyaye ya kamata su zama ga ‘ya’ yan su”. A cewar TY Shaba.