Kannywood
Gwamnatin Kano za ta gina Cibiyar Fasahar Zamani Kimanin 16.3M don inganta Kannywood
Advertisment
GWAMNATIN Jihar Kano ta kasafta kuɗi naira miliyan goma sha shida da dubu ɗari uku da saba’in da uku da ɗari shida da casa’in da tara (N16, 373,699.00) don gina Cibiyar Fasahar Zamani (Information Technology Centre) a ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai ta jihar.
Wannan bayanin ya fito ne daga sanarwa ga manema labarai wadda Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya bayar a yau.
Kwamishinan ya bayyana cewa Majalisar Zartaswa ta jihar ce ta yanke wannan ƙudirin a taron ta na mako-mako da ta gudanar a Gidan Gwamnati jiya Talata.
Mujallar Fim ba ta samu cikakken bayani kan yadda wannan cibiya za ta kasance ba, amma wata majiya ta kurkusa da gwamnatin ta faɗa mata cewar wannan wani yunƙuri ne na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na ƙarfafa hukumar da kuma sana’ar fim a jihar.
Majiyar ta ƙara da cewa yunƙurin kafa cibiyar ya biyo bayan wata shawara ne da shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya ba gwamnan kan yadda za a haɓaka harkokin shirya finafinan Hausa ta hanyar zamani.
Afakallah dai ya na daga cikin jami’an gwamnatin waɗanda gwamnan ya ke ɗaukar shawarar su don gina kyakkyawan mulki a jihar.
Majiyar ta faɗa wa Fim cewa idan an kammala gina cibiyar, za a samu damar taskace duk wani bayani na shirin finafinan Hausa, ba a Kano kaɗai ba har ma a sauran jihohin da ake yin finafinan, “saboda Kano cibiyar harkar ce.”
Majiyar ta ce, “Lokaci ya yi da dukkan ‘yan fim ya dace su ba wannan yunƙuri goyon baya domin su ne abin zai amfana a ƙarshe”.
Sai dai tun ba a je ko’ina ba wani mai shirya finafinai ya faɗa wa mujallar Fim cewa “kuɗin sun yi kaɗan”.
Furodusan, wanda ya ce a sakaya sunan sa, ya ƙara da cewa, “Mun gode wa Gwamna Ganduje da wannan abu. To amma ya sani cewa miliyan goma sha shida ba inda za ta je wajen kafa cibiyar fasaha ta zamani.
“Ya san kuɗin kayan aiki irin su manyan komfutoci kuwa? Nawa za a kashe wajen gina gidan yana, wato website, mai ƙarfin gaske wanda zai ɗauke irin bayanan da ake buƙata? Tebura da kujeru da na’urorin sanyaya ɗaki fa?
“Ɗaukar ƙwararrun ma’aikata aiki tare da horas da su fa? Bayan haka, ba za a gina ɗakunan cibiyar ba ne, a ƙawata su?”
Furodusan ya ce duk da yake an ce wanda za shi sama ya taka leda ai cigaba ne, ya kamata gwamnati ta maida kasafin gina wannan cibiya zuwa aƙalla naira miliyan 100.
Ya ce, “In dai cibiyar irin ta zamani ce, to yasin za ta ci miliyan ɗari har da ɗori. Ya kamata Afakallah ya kai wa gwamna sabon kasafi tare da ƙididdigar abin da za a kashe a zahiri.”fim magazine na wallafa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
div>
Leave Comment Here