Addini

AUDIO : Darajar Ilimi Da Abubuwan Da Suke Jawo,Zagi Da Cin Mutuncin Malamai Guda (13) ~ Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

1- Rashin ɗaukar karatu agaban malamai, se ɗauka a littattafai.
2- Mutum ya ƙone bai tafasa ba, Wato baza su tsaya suyi karatun ba Allah Allah suke suma su ɗare minbari, Allah Allah suke suma su zama masu fatawa su zama masu lakca yaƙi haƙura yayi karatu.
3- Nuna illimin Alhali babu illimin, bai ma yi illimin ba amma zai nunawa mutane shi mai illimi ne.
4- Yana dubawa a littattafai wani malamin yayi magana akan wani malamin wani malamin ma haka, maganar da su kayi da ijtihadi ko ta’awali ko Saboda wani dalili na illimi kamar Abinda muka sani (illimin jarhu da ta’adil) wanda an kafa shine domin tantance hadisan manzon Allah (s.a.w) domin ware ingantacce da wanda ba ingantacce ba Saboda haka shi idan yana karanta waɗannan sai yace to ah ai magabata sun sossoki junansu, don haka mai zai hana nima inyi suka ga wadanda muke tare dasu, wannan shima sai yaje fashi cikin wata talaɓa ɓiya da ba zai iya fita ba.
5- Wata ƙila zai ce yana kwaikwayon ibn hazm Abu Muhammad aliyu ibn hazm Azahiry, wanda littatafansa Suna ɗauke da suka ga malamai manya manya, Toshi a tarinhinsa akwai dalilai da yasa yayi haka :-
Na farko :- Yawanci karatun sa ba’a hannun malamai yayi su ba, kamar yadda Ashaɗiby ya faɗa a cikin Almuwafaƙat.
Na biyu :- Ya haɗu da ƙiyayyane mai zafi ta malaman zamanin sa, yaga bala’i iri iri, harƙona masa laburarinsa gaba ɗaya anyi, shi yasa idan ya tashi sai ya ragargaje su baki ɗaya, to kai me akayi ma a yanzu, an ƙona maka laburarin ka ne ko an matsa maka ne, don me zaka kwaikwayi ibn Hazm.
6- Jahiltar darajar wanda kake suka, matuƙar baka zauna da mutum ba, ba kayi rayuwa dashi ba, yana yiwuwar ka jahilci matsayinsa. To kaga dole ka jingi na masa Abinda ba shine ba, wata ƙila da kasanshi da ba zaka faɗi abinda kafaɗa akan sa ba.
7- Wasu Suna tasirantuwa da irin abubuwan da ke faruwa a ƙasashen yamma na turai, na damukuraɗiya da freedom of speech, musanman ma waɗanda suka rayuwa a can.
8- Ra’ayin riƙau na ƙungiyanci, saboda haka duk wanda baɗan ƙungiyar saba to baya kallonsa da daraja, Saboda haka sai ya taɓa wanda bana shi ba, Amma idan antaɓa nashi to baza’a zauna lafiya ba.
9- Hassada da rigima akan wani shugabanci.
10- Rashin tsayawa a tabbatar da abu, yayin da kaji an faɗi wani abu batare da bincike ba caraf sai ka ɗauketa kayi ta yaya tata, shikenan se a shiga sukar wanda bai jiba bai gani ba.
11- (ALFARAG) :- Rashin abunyi, zaune yake bashi da abun yi, yana da lokaci ishaishe to kuma babu abinda zaiyi, ƙarshe se kaga ya shiga abinda ya shafi giba da annamimanci da sukar wanɗanda ba suji ba basu gani ba.
12- Mutumin da ka taimaka masa ko karantar dashi mai makon ya dinga tuna Wannan wafa’i naka na cewa ka karantar dashi sai yaji bashi da wannan, duk ranar da yaji shima ya taka minbari ko ya iya tsayawa a cikin jama’a sai ya faɗa sukar ka, bacin da shi yake yabon ka.
13- Neman shuhura :- mutum yana ganin bazai sami shahara ba sai ya soki malamai, ya taka kafaɗar wani sannan a hango shi.
Domin Downloading Audio
??

DR. MUHAMMAD SANI UMAR R/LEMO, A Lakcar Dayi Akan Darajar Malamai Da Illimi A Kaduna Masallacin Al-manar.
✍? Bukhari Muhd Musa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button