ABIN TAKAICI : Raddi Mai Zafi Da Datti Assalafy Yayi Akan Wanda ya Sha Fiya Fiya Kan Maryam Yahya
Na ga wani Labari a kamfanin jaridar Rariya wai wani matashi ne yasha guba zai kashe kansa sabowa soyayyar da yake yiwa wannan yarinya da kuke gani a hoto, wata ‘yar Hausa film ce
Wato ina mamakin yadda hankalin mutanen mu ya tafi a kan mata, yanzu da zai ga wannan yarinya a zahirinta batayi kwalliya da hoda ba watakila sai ya tsani kanshi saboda muninta ga kuma bakin hali
Wadannan mata hoda ne, a cuci maza ne, ba asalin kyan fuskarsu bane, hoda ne kala-kala suke amfani dashi suna kwalliya wajen yaudaran wawaye, har da wani hoda mai suna “mai da tsohuwa yarinya”, yaushe mutanen mu zasuyi hankali ne game da makircin mata?
‘Yan matan banza ‘yan duniya da karuwai suna shafe fuskarsu da hoda suna tallata kansu a kafofin sada zumunta suna ta yaudara da damfarar garori gidadawa a kafofin sada zumunta, amma samari kun kasa ganewa?
Irin wadannan fitsararrun mata me ya rage a garesu na sha’awa, an riga da an gama da su, idon su ya bude, babu wani abun so ko sha’awa a tattare da su
Mata kamar ba ‘ya’yan Musulmai ba, sun lalace sun zama cikakkun ‘yan iska sun dena shiga ta Musulunci sai kace ‘ya’yan arna, ga shaye-shaye, menene abin sha’awa gurin wadannan fitsararru da wai har mutum zai kashe kanshi a kansu?, tarkacen banza kawai