Labarai

Yanzu- Yanzu : Shugaba Buhari Zai Dauki Ma’aikata Dudu Daya (1000) A Kowace Karamar Hukuma A Nigeria Tare Da Waƙilin Kowace Jaha

A yaune Gwamnatin Maigirma shugaban Kasa Muhammadu  Buhari Maigaskiya ta rantsar da kwamitin da zasu yi aikin samar wa mutane dubu daya (1000) a kowace karamar hukuma a Nigeria aiki, adadin da ya kai mutane dubu (774,000) a fadin Kasar wanda za’a dinga biyansu albashi Naira dubu ashirin (20,000) a kowannen karshen wata

An zabi shugabannin da mataimakan su da kuma Sakatarorin su, an fitar da jerin sunayen shugabanni kowace jiha dauke da lambobin wayar mutanen da aka dauka a matsayin kwamitin (State Selection Committees) ko SSC, wadanda zasu tafi zuwa kananan hukumomi domin kafa kwamitocin su

Ana so a fara Shirin ne ranar 1 ga watan October mai zuwa wato watan 10, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika kudaden wadannan ayyukan gaba daya ga babban bankin kasar wato CBN.

Karamin Ministan Kwadago Mista Festus Keyamo (State minister of Labour) shine ya jagoranci rantsar da mutanen, wannan shiri ne da shugaban kasa Buhari ya kawo dan rage halin da ake ciki a fadin kasar bayan cutar coronavirus ta tagayyara arzikin mutane.
Sauran bayanai game da wannan shirin zai zo nan gaba in sha Allah.

Ku taimaki shugaba Buhari da addu’ah domin ya samu nasara akan ‘yan jari hujja da maciya amana, kar ku masa tawaye, kar ku biyewa masu tunzuraku zuwa ga zanga-zanga domin ba alheri bane, kuma ba mafita bane

Allah Ka taimaki shugaba Buhari, Ka bashi ikon sauke nauyin shugabancinsa, Ka tabbatar mana da dukkan alheri a Kasarmu Nigeria Amin.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button