Addini

Bidiyo: Raddi Mai zuwa Ga Gwamnati! Babu me Gidan kajin Da zai yadda Awa kajinsa kisan Da Akewa mutanen Najeriya ~Sheikh Nura Khalid

Advertisment

Shahararren Malamin Addinin Islama, Shekih Nura Khalid yayi zafafan kalamai kan kisan da akewa ‘yan Arewa kuma an yi “Shiru”. Yace su ba zasu daina magana ba kuma koda an rufe masallatai zasu hau yanar gizo su gayawa Duniya.
Malam Nura ya bayyana hakane a Lokacin Huduba da yake a masallacinsa. Yace abin takaici ya ji daya daga cikin gwamnonin da jiharsa ke fama da ‘yan Bindiga wai ya haram ta Almajirci.
Yace Corona an mayar da ita kamar Almajirai ne suka kawo ta, ana hucewa akansu. Yace abin takaici wai sai an kashe mutane sai shugaban kasa ya fito yana cewa yayi Allah wadai. Yace ba Allah wadai ne aikin shugaba ba, mataki ya kamata ya dauka in kuma ba zai iya ba ya sauka.
Malam ya kara da cewa manyan mutane masu gidan gona ba zasu taba yadda awa kajinsu irin kisan da akewa ‘yan Najeriya ba, yace idan aka kashewa me gidan gona kaji 200 a rana daya to zai kira jami’an tsaro.
A ‘yan kwanakinnan dai ana samun karuwar hare-haren ‘yan bindiga a Arewacin Najeriya wanda hakan ke kara Munana matsalar tsaro.
Ga bidiyon nan kasa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button