Kannywood

Bazamu Iya Gyaran Kannywood Ba Sai Da Gwamnati ~ Maryam Ctv

JARUMA Maryam CTV ta bayyana batun gyaran masana’antar finafinai ta Hausa a matsayin wani gagarumin aiki wanda su da kan su ‘yan fim ba za su iya yin sa ba har sai gwamnati ta tallafa masu.

Fitacciyar jarumar, wadda sunan ta na sosai Hajiya Maryam Sulaiman, ta bayyana haka ne a lokacin da wakilin mujallar Fim ya yi mata tambaya dangane da halin ha’ula’i da masana’antar ta Kannywood ta samu kan ta a ciki a yau.

Tun da farko dai ta fara yi mana tsokaci ne kan inda harkar fim ta fara shiga mugun yanayi tun kafin zuwan cutar korona, inda ta ce, “Ita da man harkar a tsaye ta ke tun tsawon lokaci, domin kuwa yanayin da masana’antar ta shiga ne ya sa tun a shekarar da ta gabata, a lokacin kakar zaɓukan ƙasa, ‘yan fim su ka shiga harkokin siyasa, don haka sai ya zama abin bai bayyana ba.

“Amma da aka gama siyasa sai ya zama an dawo an zauna. Waɗanda su ke da kuɗi a hannu su ka koma kasuwanci, wasu su ka koma gona su ka zuba kuɗin su; duk haka dai abin ya zama.

“To kuma ana cikin haka sai wannan matsalar ta ‘Covid-19’ ta zo, wanda hakan ya dakatar da duk wasu harkoki na kasuwanci a duniya.

“Don haka dai a yanzu matsalar taɓarɓarewar kasuwanci ba wai harkar fim ba ce kaɗai, abin ya shafi duk duniya ne. Sai dai fatan Allah ya kawo mana ƙarshen wannan musifa.”

Mun yi mata tambaya dangane da matsalolin da su ke tasowa a cikin masana’antar, waɗanda an fi danganta su ga mata. Shin ko a matsayin su na iyaye mata akwai irin rawar su ke takawa don ganin an samu sauƙin matsalolin?

Hajiya Maryam ta amsa: “E to, mu na yin iyakar ƙoƙarin mu domin ganin an samu sauƙin wannan al’amarin. To sai dai abin da ya kamata mutane su sani shi ne gyaran harkar fim mu kaɗai ba za mu iya ba, sai hukuma ta shigo ciki.

“To amma a yanzu alhamdu lillahi, mu na ganin za a samu nasara tunda hukumar ta ɗauki mataki, domin kuwa idan ka kula Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, a ƙarƙashin Afakallahu, sun fito da hanyoyin da za a samu sauƙin irin waɗannan matsalolin da ake fama da su. Domin kuwa tsarin tantancewar da ake yi zai taimaka sosai wajen rage matsaloli, musamman ma na yara mata.

“Saboda haka a yanzu duk wanda ya ke son ya shigo masana’antar sai ya bi ta tsarin da aka saka wanda shi ne zai sa a gane su waye ‘yan fim na hakika, su waye kuma masu yin sojan gona.

“Yanzu in ban da yanayin nan da aka shiga na ‘Covid-19’ da tuni shirin ya yi nisa.

“To ka ga abin ya na da kyau. Da yardar Allah nan gaba za a samu masana’antar finafinai ta Kannywood cikin tsari, ba kamar yadda aka san ta a baya ba.”

Daga ƙarshe, fitacciyar jarumar, wadda ta na ɗaya daga cikin manyan mata a Kannywood, ta yi fatan Allah ya sanya darasin da aka samu a cikin faruwar wannan cutar ta korona ya zama alheri ga masana’antar da ma duniya baki ɗaya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button