Labarai
An Daura Auren Dan Marigayi Sheikh Ja’afar Kano Salim Ja’afar Mahmud (Hotuna)
Babban dan Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, Salim Ja’afar Mahmud Adam ya yi aure.
An daura auren yau a Abuja karfe 10 na safe .
Wanda ya daura Auren Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau da Sheikh Dr kabiru Haruna Gombe .
Wanda ya karbi Auren a Madadin Ango Shine Dr Bashir Aliyu Umar Babban limami a Masallacin Alfurqan dake Unguwar Nasarawa a garin kano . An samu halartar jama’a daga sassa daban daban daga Nigeria . Duk da an takaita taron saboda yanayin da ake ciki na covid 19 . Allah ya basu zaman lafiya .
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com