Labarai

Zantawar Dr Mansur Sokoto Da Wani Dalibinsa Da ke Dauke da Cutar Korona A Sokoto

Na zanta da wani dalibina da Allah ya jarabta da kamuwa da wannan cuta ta Covid-19. Yana nan Amanawa, Sokoto inda aka killace masu wadannan bayin Allah. Cikin abinda na tambaye shi: “Kuna da yawa, kuma kuna samun kulawa?”. Amsar da ya ba ni ta yi mani dadi kwarai. Ga abinda ya rubuta:

Eh, munada yawa, kuma gaskiya idan ban yabawa gwamnati ko’inaba anan zan jinjina mata. Nidai nikadai nake a dakina. Akwai wuta 24hrs, da toilet da ruwa ko yaushe. Akwai likitoci isassu kuma idan kanada damuwa akwai intercom da zaka kira likita yazo. Akwai abinci akwai masuyimaka shara da moping. Duk jahar sokoto babu dakin jinyar dayakai wannan tsabta.”.

Shawarata:
Mu ci gaba da ba gwamnati hadin kai game da duk wani kokari akan yakar wannan cuta, kuma mu ci gaba da daukar matakan kariyar kai. Bahaushe ya ce, lafiya ta amfani mai ita.
Wadannan yan uwan namu Allah ya ba su lafiya. Wadanda suka cika kuma Allah ya jikan su.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button