Zaman banza ya kare a Nijeriya: Buhari zai dauki mutum 774,000 aikin yi a duk fadin Nijeriya
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti da zai samarwa yan kasa 774,000 ayyukan yi na musamman domin magance talauci da zaman kashe wando a duk fadin kasar.
Kwamitin da karamin ministan kwadago da nagartar aiki, Festus Keyamo, ya kaddamar zai samu jagorancin babban daraktan cibiyar ayyukan yi ta kasa, Mohammed Nasir Ladan Argungu.
Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami, ya bayyana kokarin da gwamnatin tarayya ke yi a matsayin fitar da kimanin yan kasa milliyan 100 daga kangin talauci.
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Ayuba Wabba, ya yaba da kokarin gwamnatin ganin irin halin kunci da duniya ke ciki, tare da fatan hakan zai taimaka wajen kawar da fadawa ayyukan ta’addanci.
Daraktan cibiyar dake sa ido da kuma yaki da cin hanci da rashawa ta CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, na ganin idan har gwamnati ta cika alkawarinta wajen samarwa da ‘yan kasa ayyukan yi, tabbas zai taimaka a yankunan karkara da ma fadin kasar baki daya.
Sai dai ya nuna jimaminsa kan abin da ya ce “Cin hanci da rashawa ba zai iya bari ayi hakan ba.”
A yayin gudanar da aikin, kwamitin zai samar wa mutane akalla dubu daya aiki a kowacce kananan hukumomin Najeriya 774, inda gwamnatin za ta rinka biyansu albashin Naira 20,000 a kowanne, kamar yadda VOA ta rawaito.