Labarai

‘Yan Nijeriya Za Su Fara Biyan Kudin Wutar Lantarki Mai Yawa A Shekarar 2021, Cewar Gwamnatin Tarayya

Advertisment

Daga Comr Abba Sani Pantami

‘Yan Nijeriya za su biya karin kudin lantarki mafi yawa a cikin shekara mai zuwa, ta hanyar alkawuran da gwamnatin Tarayya ta yi wa asusun ba da lamuni na duniya, a yayin da gwamnatin Nijeriya ta nemi taimakon dala biliyan $3.4 cikin gaggawa kwana nan, kamar PUNCH ta ruwaito.

Kwamitin Zartarwa na IMF ya amince da tsarin Rapid, wanda Gwamnatin Tarayya ke shirin yin amfani da shi don magance tasirin tattalin arziki da matsalolin cutar COVID-19 a kasar, a ranar 28 ga Afrilu.

Daya daga cikin alkawurra, ko kuma alkawurran da gwamnatin ta yi a kokarin ta na tabbatarwa da hukumar zartarwa ta IMF a shirye ta ke ta sake fasalin tattalin arzikin Najeriya bayan barkewar cutar, ita ce cewa ‘yan Najeriya za su biya cikakken kudin alawus  na wutar lantarki a shekarar 2021.

A ranar 4 ga watan Janairu, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta amince da kara kudin jigilar wutar lantarki ga kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 a Najeriya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button