Tsohuwar Jaruma Wasa Hausa Faty Ladan, Ta Tallafa ma mata, marayu, Da marasa Galihu.
Daga Bashir Iliyasu Galma,
Ayaune 6, ga watan May, 2020, wanda yayi daidai da 12 ga watan Ramadan, tsohuwar yar wasan hausa, firm, wato Faty ladan. Mata ga Yerima Shettima, shugaban kungiyar Arewa Youth Consultative Forum, tayi Rabon tallafin kudi,, a Hayin Danmani dake cikin garin Kaduna, ga Mata marasu karfi da tsofaffi da kuma, marayu.
A Jawabin ta a “”wajen rabon tace tayi ne Dan ganin halin da al’uma suka shiga na Rashin kudi ga matsalan da kasa take ciki na cutar Coronavirus, da ya dakatar da kusan ko wani harkoki na yau da kullun, inda hatta neman abinci, wasu basa samun damar da zasu fita don neman abinda zasu ciyar da Iyalan su.
Hajiya Faty Ladan, ta takara da jan hankalin ilahirin mahalarta taron dama sauran Jama’a baki daya cewa tabbas wannan cuta ta Corona virus, gaskiya ce dan haka su kauracewa duk abinda ze kaisu ga kamuwa ga wannan cuta, ta hanyar bin shawar,warin likitoci masana harkar lafiya, tare da bin dukkan dokokin da Hukumomi suka sanya; domin daqile yaduwar wannan cuta.
“” bayanin hakan ya fito ne daga bakin Comr. Mubarak Ibrahim Lere, akarshe tayi addu’a wanda suka kamu Allah ya basu lafiya, wanda kuma basu kamu ba Allah ya karesu.