Shugaban Buhari Ya Bada Umarni A Gama Da Yan Ta’addan Da Suka Addabi Katsina
Daga : Datti asaalafy
Maimagana da yawun shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya Malam Garba Shehu ya fitar da sanarwan cewa shugaba Buhari ya bada umarnin daukar matakin soji a kan ‘yan ta’addan da suke ta’addanci a jihar Katsina
An tura rundinar sojoji mayaka na musamman kwararru cikin sirri zuwa wasu manyan sansanin ‘yan ta’adda da aka gano a jihar Katsina. a sanarwan da Malam Garba Shehu ya fitar, kuma yakin zai kasance cikin sirri ne
Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa da matukar damuwa bisa halin da aka shiga na tabarbarewan tsaro a jihar Katsina, ya bawa sojoji umarni su kakkabe dukkan wata maboya na ‘yan ta’adda a jihar, yakin zai kasance da taimakon sojojin kasa da sama da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro
Muna rokon Allah Ya sa wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka ya zamto sanadin kawo karshen ta’addancin da akeyi a jihar Katsina