Addini
Mai Martaba Tsohon Sarkin Kano Mal Muhammadu Sanusi II yayi Raddi Ga ‘Yan Boko Aqeedah
Advertisment
A karatunsa na jiya, wanda yake gudana cikin littafin “Madaarijus Salikeena”, Mai Martaba ya karanta tambaya da aka yi masa inda ya ce:
“Akwai Tambaya a kan hukuncin wanda ya zagi Manzon Allah (saw)?
(Amsa):
Mai Martaba Sarki yace:- “Wanda iyakacin fahimtata, duk Malamai sun taru a kan wanda ya zagi Manzon Allah (saw), hukuncinsa hukuncin kisa ne, Ibn Taimiyya yana da littafi guda da yayi mai suna “Assaarimul Maslool ‘ala Shaatimir rasool” inda ya kafa hujjoji kan wannan”.
Domin karin bayani a saurari Lecture na 9 Video Muhammad Sanusi II’s Family Study Group (01 May 2020)
Allah Ka sakawa Maimartaba Sarki Malam Muhammad Sunusi II da alheri, Allah Ka kara masa lafiya da imani Amin
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com