Kannywood

Maganar Gaskiya Shin Yan Sanda Sun Kama Musa mai Sana’a ? – Musa Mai Sana’a

Advertisment

A yammacin wannan rana ta juma’a wani labari ya ke ta yawo a soshiyal media, inda a ka ruwaito cewar, sakamakon karya dokar hana taron Sallar juma’ a a Kano, hukumar ‘yan sanda ta kama fitaccen jarumi, Musa Mai Sana’a saboda ya jagoranci Sallar juma’a a wannan ranar, domin haka jami’ an tsaro su ka damke shi.

Da farko dai labarin ya fara kamar wasa, amma zuwa dan wani lokaci sai labarin ya cika gari a na ta yin sa.

Domin jin hakikanin yadda labarin ya ke, wakilin mu ya kira Musa Mai Sana’a ta waya, inda ya ke tambayar sa ko me ne ne gaskiyar kamun da a ka ce hukumar ‘yan sanda ta yi masa a sakamakon Jan Sallar juma’a da ya yi?

Sai ya amsa da cewar “To wannan labarin ba gaskiya ba ne, domin ni ba Malami ba ne kuma ba ni da wani masallaci da na ke jan Sallah, domin haka wasu ne dai kawai su ka hada labarin, saboda wata manufa, amma dai maganar gaskiya ba a kama ni ba, domin yanzu maganar da mu ke yi da kai idan ka na son mu hadu da kai sai ka fada min duk inda ka ke na zo na same ka, domin ka tabbatar da gaskiyar maganar, don haka ina nan ban yi wani laifi da har za a kama ni ba, ni mai bin doka ne don haka babu yadda za a yi na samu kaina a cikin ma su kin biyayya da abun da hukuma ta zartar domin neman maslahar jama’a”. Mai Sana’a.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button