Labarai

Maganar Gaskiya Akan Jita Jita Da Ake Yadawa Cewa Malam Aminu Daurawa Ya Rasu _ Daga Ɗansa Huzaifa Aminu Daurawa

Wannan shine bayyanin da ɗansa Huzaifa aminu daurawa na wallafa.

Jita-jita da ake yadawa cewa Malam ya rasu aba ce da wasu suka kirkiro Allah shi ya san manufar su
Malam yana samun lafiya sosai bal ko a yau din nan ya kara samun sauki akan jiya, kusan kullum yanzu kara samun sauki yake yi Alhamdulillah

Annabi SallAllahu-alaihi-wasallam yayi gargadi akan azabar da za a yiwa Wanda yake karya ta yada duniya, a lokacin da Annabi SallAllahu-alaihi-wasallam ya Fadi hadisin ana dadewa kafin labari ya yada duniya, Amma yanzu cikin seconds yake yaduwa, Ashe yanzu ya fi kamata mu yi taka tsantsan

Idan kana so ka tabbatar da ingancin duk labarin da ya shafi Malam a social media ga wasu daga cikin shafukan da za ka duba

Akwai Shafin Malam me suna Mal.Aminu Ibrahim Daurawa, a wannan shafin Malam yake live videon sa kuma shine official shafin sa
Akwai account di na Huzaifah Aminu Daurawa, da account din kani na Usama Aminu Ibrahim
Akwai account Umar Bin Khamis wanda shi yake recording din programs na Malam

Allah ya kara ba wa Malam lafiya ya kiyaye shi daga dukkan abun ki”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA