Labari Mai Dadi ! Za a cigaba da sallar Juma’a a Masallatan jihar Jigawa
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da ya ke sanar da sallamar da masu jinyar korona 7 da aka sallama daga cibiyar killacewa ta jihar Jigawa bayan an tabbatar sun warke sarai.
Ya sanar da hakan ne yayin taro da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
A cewar gwamna Badaru, ya amince da bude Masallatan ne bayan ganawarsa da kungiyar malamai ta jihar Jigawa.
Ya ce sun cimma yarjejeniyar cewar za a bi dukkan matakan dakile yaduwar kwayar cutar korona a Masallatan.
Gwamnan ya ce dole a yi wa matakan dakile yaduwar cutar korona biyayya saboda masana sun yi hasashen cewa mutane 800 zuwa 20,000 zasu iya kamuwa da kwayar cutar a jihar Jigawa idan ba a kiyaye ba.
Badaru ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kammala shirin samar da cibiyar gwajin kwayar cutar korona wacce za a iya gudanar da gwaji 180 a rana.
A cewarsa, cibiyar, wacce za ta fara aiki a cikin sati biyu masu zuwa za ta kawo karshen wahalar daukan samfurin jini daga Jigawa zuwa wasu jihohin domin gudanar da gwaji.
Gwamna Badaru ya ce ya zuwa yanzu an tabbatar da samun mutane 118 da ke dauke da kwayar cutar, yayin da annobar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.
Ya kara da cewa kaso 53% na wadanda ke dauke da cutar a jihar Jigawa almajirai ne da aka dawo da su daga jihar Kano.
A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, kwamitin kar ta kwana a yaki da annobar korona a jihar Gombe ya sanar da cewa an sallami masu jinya 39 daga cibiyar killacewa bayan sakamakon gwajinsu ya nuna cewa yanzu basa dauke da kwayar cutar.
Ya zuwa yanzu an sallami jimillar mutane 39 daga cibiyar killace masu dauke da kwayar cutar korona a jihar Gombe.
Shugaban kwamitin, Idris Mohammed, ya bayyana cewa an sallami mutane biyar ranar Litinin, yayin da aka kara sallamar wasu 34 ranar Talata bayan sakamakon gwajinsu da aka aikawa NCDC ya nuna cewa basa dauke da kwayar cutar korona.
Ya ce, a karo na farko, an sallami masu jinyar korona 20 daga cibiyar a ranar Asabar din da ta gabata. Sannan, ya kara da cewa an sallami jimillar mutane 59 da yanzu haka sun koma cikin iyalansu.
#legi