Kowacce Cuta Da Maganinta ! Hanyoyin Karfafa Garkuwar Jiki
Ai Sharin Dan Allah Yan uwa
Garkuwar jiki wasu kwayoyin halittane wadanda suke yakin duk wataa kwayar cuta da ta shigo jikin mutum. Idan kwayoyin cuta suka fi karfin garkuwar jiki mutum sai su nakasa garkuwar jiki dagan kuma sai mutum ya kamu da rashin lafiya cikin ikon Allah. Akwai hanyoyi dayawa da akan be wajen karfafa garkuwar jiki, don samun kariya daga kamuwa da cuttuka, ga wasu daga cikin hanyoyin kamar haka;-
HANYA TA FARKO
Arika shan ruwan dumi da safe tun kafin aci komai Kofi daya sai Kuma bay minti arba’in da biyar (45) aciki abinci. Yin hakan na karfafa garkuwar jiki sosai.
HANYA TA BIYU
Shan ‘ya’yan itatuwa kamar , lemo, ayana, gwanda, apple, abarba da sauransu sukan karfafa garkuwar jikin mutum.
HANYA TA UKU
Busassun ‘ya’yan itatuwa kamar , magarya, kurna, aduwa, taura, goruba da sauransu, suma sukan karfafa garkuwar jikin mutum.
HANYA TA HUDU
Ganyayyaki kamar irin su,
alayyahu, latas, lansir, yakuwa, zogale, rama, yadiya, kabeji da sauransu, suma sukan karfafa garkuwar jikin mutum.
HANYA TA BIYAR
Garin Habbatus-sauda ko man Habbatus-sauda na asali marar hadi, shima yana karfafa garkuwar jiki mutum, idan mai ne sai arika Shan cokali daya acikin ruwa dumi ko shayi sau biyu arana. Idan kuma garin ne sai arika dafa cokali biyu acikin ruwa kofi daya atace azuba zuma agarwaya asha kofi daya sau biyu arana.
KARAIN BAYANI
Amma kar mace mai ciki tayi amfani da hanya ta biyar wato man Habbatus-sauda ko garin Habbatus-sauda, sai cikin nata yakai wata 3 zuwa sama.