Addini

Ko Ka So, Ko Ba Ka So Ba Sai Mun Jagoranci Sallar Idi A Kaduna, Sakon Sheikh Abubakar Salihu Zaria Ga Gwamna Elrufai

Shahararren malamin addinin musuluncin nan na kungiyar Jama’tu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Abubakar Salihu Zaria, ya ce sun gaji da mulkin kamakaryar da gwamna Nasir el-rufai ke yi a jihar Kaduna, a don haka za su yi sallar Idin bana ko gwamna ya yarda ko bai yarda ba.

Sheikh Abubakar, yayi wannan alwashi ne yau a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Hausa7 Nig ta wayar tarho, inda ya ce “Ku rubuta ku sanar wa al’ummar jihar Kaduna cewar; ni Abubakar Salihu Zaria, na ce su fito ranar sallah zan jagoranci sallar Idi ko da gwamna el-rufai ba ya so”

Idan dai ba’a manta ba, Gov. el-rufai, ya sanya dokar hana zirga-zirgar al’umma ne sakamakon bullar cutar Corona virus a jihar Kaduna, inda gwamnatin sa ta ware ranakun Laraba da Asabar a matsayin ranakun da aka bawa al’umma damar fita su yi siyayyar kayan abinci, daga baya kuma gwamnan yace ya soke fitar al’umma ranar Asabar wacce kuma ake tunanin ranar ce al’ummar musulmi za su yi sallar Idi.

Ko a kwanakin baya ma Sheikh Abubakar Salihu Zaria, ya sha hawa Mimbari da sauran wuraren wa’azozin sa yana kalubalantar Gov. el-rufai game da yadda ya kori ma’aikata sama da mutum dubu 23,000 a fadin jihar Kaduna.

#Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button