Irin Zaman Amana Da Muka Yi Da Marigayi Ubale Ibrahim, Cewar Yakubu Muhammad
“Allah ya ji kan ka Ubale. Mun yi babban rashi. Muna bude baki ya kira ni, muka yi magana akan da safe zamu hadu.Ya yi sallar Isha, sun ci abinci da abokan sa a unguwar su, ya yanke jiki ya fadi,ashe tafiyar kenan. Mai dakin sa ta kira mu sai asibiti, muna isa Doctors suka ce ai ya rasu. Innalillahi wa inna ilayhir raji’un.
Ubale ya girme mu ni da Sani amma ya kasance a sana’ance a kamfanin mu yake. Duk abinda ka sa shi ba girman kai ba dagawa zai je yayi. Wanda bai kai shi ba ma sai ka ga ya sa Ubale aiki ko kuma ka ga ya aike shi kuma ka ga ya je. Ubale a wajen marigayiya mahaifiyar Sani Danja ya girma, duk da ba ‘yan uwantaka na jini, unguwa ce kawai ta hada su, sai da ya zama kamar ita ta haife shi.
Idan aka nemi Sani ko Yakubu bama nan, to Ubale shine wakilin mu. A dawainiyar mu bai taba nuna gazawa ko kosawa ba. Ya yi dawainiya damu da ‘ya’yan mu. Duk inda na je Ina shigowa Kano shi nake fara kira a waya. Ya girme ni amma Yallabai yake ce min. Sai ka ji yace ‘Yallabai gani nan zuwa’. Ko mai yake zai bari ya zo inda nake.
Dole ne in yi kuka, Ubale ya sha wahala sosai.
Shekarar da ta gabata daidai wannan lokacin (azumin bara) Hawan jinin sa ya tashi har sai da ya samu matsala a kwakwalwa kusan wata guda ba ya iya gane komai, hatta iyalin sa da ‘ya’yan sa. Muka yi ta magani har Allah ya ba shi lafiya. Sau tari ba shi da kudi, babu abinci da za su ci a gidan sa, amma ba zai taba bude baki ya ce ga halin da gidan sa yake ciki ba, sai dai in mun lura da yanayin sa mun tambaye shi sannan zai fada mana a magance masa matsalar.
Bai damu da abin duniya ba. Idan na dame shi da bai son kazar -kazar wajen neman kudi sai ya kalle ni ya yi murmushi ya ce Yakubu kenan…
A koda yaushe yana mai godiya ga Allah da dan abin da ya samu. Ubale kwalliya da riga basu dame shi ba. Idan yayi wata shigar sai na yi ta masa surutu ince kai fa jarumi ne, television star, ya kamata ka dinga yin gayu sai ya yi dariya yace Yakubu kenan. Ko Ubale ya yi fushi lokaci kankani za ka ga ya huce komai ya wuce. Haihuwar sa na farko ya yi min takwara. Ya sa wa jariri Yakubu. Yanzu Yakubu ya kai shekaru 17.
Madogara facebook/Rariya