Addini
Ina godiya Da Addu’o’in Da kuke min:Ina sanar daku cewa ina samun sauki sosai>>Sheikh Daurawa
Advertisment
Shehin malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya mika godiyarsa ga ‘yan uwa da suke sakashi cikin addu’o’in su inda yace yana godiya sosai.
Malamin wanda a baya saboda rashin lafiyar da yayi, wasu suka rika yada cewa ya mutu,amma daga baya ya fito ya karyata, yace yana godiya da addu’a.
Sanarwar ta fitone daga shafin Malam Na facebook inda yace:
“Assalam alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barakatuh, Muna godiya ga yan uwa masu albarka na nesa da na kusa, bisa ga addu’o’i da suke yiwa malam domin samun lafiya. Muna sanar da ku cewa malam yana godiya, kuma yana kara samun sauki da izinin Allah.”
Muna fatan Allah ya baiwa Malam Lafiya
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com