Uncategorized

Hukuncin Kaciyar Mata A Musulunci

TAMBAYA TA 2753
*******************
Assalamu alaikum malam ina fata kana cikin koshin lafiya Allah yasa haka amin malam Allah ya azurtani da samun ya mace kasancewar abaya duk yayan da nake haifa maza ne kuma ba’a cire musu abun wuya to ita ma mace za’ai iya barinta batare da ancire mata abun fa ake cirewa a gaban su ba? Ina fatan malam zai amsa mini wannan tambaya tawa domin ina fuskanta matsin lamba daga wajan matata amma idan taga abun da kace to zata yarda .
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Shi yiwa mata kaciya, yazo a wasu hadisai cewa Manzon Allah ﷺ yace “Yiwa mata kaciya, girmamawa ce”.
To amma wasu maluman sun ce kusan dukkan hadisan dake magana akan kaciyar mata din, dha’ifai ne (wato raunana) babu ingantacce daga cikinsu ko daya. (Kamar yadda Shaikh Sayyid Sabiq ya fa’da acikin Fiqhus Sunnah, babin dake magana akan kaciya). Sai dai kuma ai ba’a hana yin aiki da raunanan hadisai ba, musamman acikin abinda ya shafi riskar wata falala, ko wa’azantarwa.
Don haka ma Maluman fiqhu suka daukeshi amatsayin mustahabbi. Shi kuma kaciyar maza wasu malaman Mazhabin Zahiriyyah sun ce wajibi ne. Amma  Imamu Malik da mafiya yawan Malaman Shafi’iyyah sun ce sunnah ne.
A bangaren likitocin Musulunci kuma, wasu daga cikinsu sun ce lallai yiwa mata kaciya din nan yakan sanya hasken fuska da ni’ima garesu kuma yakan rage musu Qarfin sha’awa alokacin budurci. Wanda kuma wannan din abu ne mai kyawu saboda yakan taimaka wajen kiyaye mutuncinsu.
Hakanan Ibnu Qudamah Almaqdisiy acikin littafinsa “Al Mughnee” ya kawo hujjoji akan sunnancin yin kaciya ga mata, kuma ya dogara da sahihiyar fatawar Imamu Ahmad bn Hanbal akan haka.
Don haka abinda nake gani shine : ka barsu suyi mata kaciyar, amma ka sanya ido sosai akan lamarin. Ka gaya musu suyita sama-sama (kamar yadda Annabi ﷺ ya bada shawara ga wata wanzamiya) sannan suyi amfani da sabuwar reza mai tsafta.
WALLAHU A’ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (29/05/2020).

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button