Kannywood

Babu Wanda Ya Danne Ni A Fagen Waƙa – Abubakar Sani Dan Hausa

ABUBAKAR Sani, shahararren mawaƙin Kannywood, ya na daga cikin mawaƙan da harkar fim ba za ta taɓa mantawa da su ba. A baya muryar sa ta sayar da finafinan Hausa masu yawan gaske.

To sai dai tsawon lokaci ba a jin sa ko ganin gilmawar sa a industiri. Hakan ya sa wasu ke ganin kamar ya bar fagen waƙar.

Don jin abin da Abubakar ya ke ciki, mujallar Fim ta tattauna da shi, inda ya tabbatar mata da cewa shi fa har yanzu ana yayin sa kuma babu wani abu da ya kwantar da shi. Ya ce ya dai koma wani ɓangare ne ya na ci gaba da waƙar.

A cewar Abubakar, a yanzu ba sai ya yi waƙa a fim zai ci abinci ba. Ya ce: “To ni dai ina ganin duk wani mawaƙi da ya taso a yanzu ban yi lokaci da shi ba, kuma bai danne ni ba, don ni ba zan dannu ba.

“Har yanzu ina nan ina girgiza rawa da baza ta, sai dai na yi ƙoƙari na inganta basira ta da Allah ya ba ni, ba kamar yadda a baya mu ke ta sakin ta kawai ta tafi a banza ba.

“Domin kuwa duk abin da ya yi yawa a kasuwa to darajar sa za ta karye, kuma duk abin da ya yi ƙaranci za ka ga darajar sa ta yi sama.

“Yanzu ka ga ana sauraron waƙoƙi na na shekaru sha biyar da su ka wuce. To, da ina yin sababbi, da tuni waɗannan sun ɓata. Ni kuma kullum ina ƙoƙari na in yi dashe ya girma, yadda ba ni kaɗai ba har wani ma ya ci.

“Don haka maganar ko waƙa ba ta yi da ni ba ta taso ba, don ita harkar waƙa mu na dai ‘mawaƙan finafinan Hausa’, domin ba zan raina harkar ba, da ita mu ka fara, to amma dai ba sai na yi waƙar fim na cika mawaƙi ba. Akwai hanyoyin da zan bi in ci da waƙa, kuma su na da yawan gaske, don a baya harkar waƙar fim neman suna na yi da ita, yanzu kuma harkoki na da na ke yi neman kuɗi na ke yi.”

Shahararren mawaƙin ya ci gaba da cewa, “Ka ga yanzu ina tallar kamfanoni, ina yin waƙoƙin siyasa, ina yin na faɗakarwa, wanda zan ɗauki wani abu na yi waƙa a kan sa domin faɗakarwa.

“Sannan yanzu so na ke waƙoƙi na su shiga ƙasashen duniya, don a yanzu na gama da Afirka, na fara shiga duniya. Idan ka hau Intanet za ka tabbatar da hakan, duk da ba ni na ke sakawa ba a baya, amma a yanzu ina sakawa da kai na, domin masoya waƙoƙi na a duniya su rinƙa samun su cikin sauƙi.

“Don haka har yanzu ana yayi na, kuma za a ci gaba da yayi na a fagen harkar waƙa.”

Daga ƙarshe, Abubakar Sani ya yi kira ga abokan sana’ar sa ta waƙa da cewa lallai su sani ita waƙa ba za ta yi tasiri ba sai mutum ya na da ilimi, don haka mawaƙan su tashi su nemi ilimi, musamman ma dai na waƙar da su ke yi. Ya ce idan kuma ba haka ba, duk yadda ka iya waƙa ka na ji ka na gani za a bar ka a baya, sai dai kowa ya zo ya wuce ka.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button