Ba Zan Halarci Taron Goyan Bayan Hana Sallah Ba A Kaduna, Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun
Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano
Mataimakin shugaban majalisar malamai ta Kasa na kungiyar Izalah kuma daya daga cikin manyan malamai a jahar Kaduna, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce ya ki halartar taron da aka yi da malamai a gidan Gwamnati na jihar Kaduna a jiya saboda ba zai goyi bayan hana sallar jama’a da sallar idi ba.
Ya ce duk taron da zai sa ya goyi bayan hana sallah ba zai halarce shi ba
“Ban ga dalilin da zai sa a bar mutane suna halartar kasuwanni amma a hana su zuwa wajen bautar Allah da ba zai wuce minti 30 ba. Haka kuma ban ga dalilin da zai sa na goyi bayan Gwamnati ba akan hana sallah, cewar Sheik Yusuf Sambo Rigachukun.
Sheikh Rigachikun ya yi wannan jawabin ne a gidansa dake garin Rigachikun bayan kammala karatun da yake gabatarwa a kullum a gidansa.
#Rariya