Kannywood

B A B U A L A Q A (saita musulunci)Falalu Dorayi Yayi Martani Mai Ban Mamaki Kan Gwamnatin kano

Advertisment

Ban san su ba, ba su sanni ba
Hasalima a siyasa ba hannun mu daya ba.

Amma lallai abin da sukai akan Yan kasuwar kano yai min dadi, kuma abin a yaba ne.

Mummunar dabi’ar nan ta Yan kasuwar mu, wato ajjiye kayan abinci da boye su,
Da jiran lokacin da aka fi bukatar su a dauko su a kara musu kudin tsiya.
Ba tare da la’akari wane hali al’umma suke ciki ba. Haka za’a siyar.
Saye ko bari.

Kuma hakan yafi faruwa a lokacin da Al’ummar musulmi suke kokarin shiga ibadar azumi, ko kuma lokacin da aka tsinci kai a cikin wani hali ko masifa.
Lokacin rashin imanin wadannan Yan kasuwa yake tashi.

Alhamdulillah nayi farin ciki da abin da wannan Hukuma tayi a kano.
(Kano State Public Complaints and Anti-corruption Commission.)
A kokarin ta na tsaftace da kuma Kawo sauki da daidaito tsakanin Talaka da masu saida kayan bukatun yau da kullum. Sunyi wani kyakkyawan yinkuri cikin kwanakinnan Hukumar wadda wani haziki (Muhuyi Magaji Rimingado) ya ke shugabanta, sunyi sumame cikin kasuwanni kano da manyan kantunan saida kaya, da kuma ma’adanar ajjiye kayayyaki. Sun bankado kaya da aka boye, da wadanda aka karawa kudi ba gaira babu dalili. Ance a take Hukumar ta dauki mataki.

Sannan sunyi zaman GA NI GA KA da Yan kasuwar, tare da ba su Umarnin sauko da kayan da suka karawa kudi, zuwa tsohon price din da kayan yake a baya. Kuma ance hukunci take ya fara aiki, bisa amincewar Yan kasuwar.

Sannan ance Muhuyi Magaji yace:
“Muddin muka tsinkayi kayan abinci da zummar ka boye shi wallahi zamu garkame shagon kuma mu kwashe kayan muyi awan gaba dashi.”

Mu musulmi yana da kyau mu zamo masu tausayi ga yan uwanmu, ta fanni wajan saye da sayarwa. In dai muna neman albarka a cikin dukiyarmu. Amma kara  kudin kaya babu dalili zalinci ne.

Ganau da jiyau da wadanda suka je domin tabbatarwa, sun iske hukuncin ya fara aiki kamar yadda aka ambata a kafafen sadarwa. Alhamdulillah.

Wannan ba Karamin kyakkyawan yinkuri bane tsakanin shugabanni da talakawan su. Allah yasa hakan ta kasance a kasa baki daya. Amin.

@kano_anticorruption
#Kano
#falaluadorayi

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button