Addini

Aya Cire Tsoro ! Sheikh Dr Abdallah G/Kaya Na Rokon Gwamnati Ta Bada Ayi Sallar juma’a

Shahararren Malamin addinin Musulunci Sheikh Dr Abdullahi Umar Usman Gadon-kaya yana mai rokon gwamnati da ta bada dama a fita sallar juma’a kamar yadda suka bada dama a fita kasuwa, banki, da sauran gurare masu muhimmanci

Sheikh Yace: tabbas sun yarda da duk sharudan da gwamnati ta kafa kuma tabbas Coronavirus gaskiya ce, amma tunda likitoci sun bada damar a fita ayi yini guda a neman abinci bisa babin lalura; to dan Allah itama sallar juma’ah lalurace a garemu musulmai

Yace: in har gwamnati tace kada a wuce minta 20 a sallah insha Allah baza a wuce ba, kuma za’a bi ka’idoji na sanya abin rufe fuska (mask) tare da bada nisan tazara tsakanin Masallata

Daga karshe yace wannan ra’ayinshi ne, kuma fahimtarsa ce, da fatan za’a masa kyakkyawar fahimta?

‘Yan uwa Musulmai mu isar da wannan sakon ya isa ga inda ya dace ta hanyar sharing da copy and paste

Yaa Allah Ka yaye mana wannan masifa, Ka bamu mafita na alheri Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button