An raina masu waka da fim a arewacin Najeriya – Ali Jita
Fitaccen mawakin Hausar nan, Ali Jita ya ce a arewacin Najeriya ba a dauki mutane irinsa a bakin komai ba, inda ake daukar mawaki da dan fim a mutanen banza.
Ali Jita ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da shafin Hausa na BBC Instagram inda ya ce “ana yi mana wani irin kallo na mutanen da ba su da makoma.”
Ya kara da cewa “yanzu ma za ka ga mawakan sun fara yin wake da Turanci domin janyo hankalin wadanda ba sa jin Hausa.
Wasu Hausawan ma wai ba sa son su saurare mu har ma suna nuna ba sa jin Hausar.”
Dangane kuma da wakokinsa, Jita ya ce kawo yanzu bai san iya adadin wakokin da ya yi ba amma dai yana da kundin wakoki da ake kira Album kamar 10.
A ina Ali ya samo lakabin Jita?
Fitaccen mawakin ya ce “tun ina dan yaro ne nake yawo da jita, har kuma lokacin da na fara shiga studio domin waka.
A lokacin da na shiga studio na ce a yi min kida da jita ne saboda ita ce na fi so a wannan lokacin ne Adam Zango ya sa min suna Ali Jita.”
Dangane kuma da wace wakar ce Bakadammiyarsa, Jita ya ce ba shi da Bakandamiya guda daya illa dai duk lokacin da ya yi wakar da ta burge shi ko kuma ta shiga kasuwa sosai ta kan zama Bakandamiyarsa.
Sai Jita ya ce ya fara waka ne tun yana makarantar Islamiyya inda ya zamo jagaban masu wake a makarantar.
Bayan waka wace sana’a Ali Jita yake yi?
Ali Jita ya ce “kamar yadda na fada a cikin wakata ta Labarin Duniya cewa idan waka tai karewa to fawa naka komawa. Mahaifina sana’ar fawa yake yi.”
To sai dai duk yanzu sana’ar wakar ba ta barin Ali yin sana’ar fawar, ya ce “ko dazu ma sai da na soka tsire muka ci ni da abokaina. Ina ma shirin bude wuraren sayar da nama amma na zamani.”
Daga karshe Ali Jita ya ce abincin da ya fi so shi ne Dan wake.