Abinda Yasa Kunka Daina Jin Duriyata – Zuhailat Ibrahim Zpreety
An shafe tsawon lokaci ba a ganin fitacciyar jaruma, Zulaihat Ibrahim Zpreety a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, wanda hakan ya sa mutane su ka yi ta tambayar ina jarumar ta shiga?
Tambayar ba ta zo da mamaki ba, musamman idan a ka duba yadda jarumar ta ke gudanar da rayuwar ta a daidai lokacin. Domin kuwa ta shigo sahun jaruman da a ke ji da su, sai dai kawai a ka daina ganin ta, duk da maganganun da ba a fada ba dangane da rashin ganin na ta, duk da wasu na cewa rashin lafiyar ta kalau ko asiri a ka yi mata ta bar harkar, wasu kuma su ce ai ta na cikin wani yanayi ne na rashin lafiya.
A wancan lokacin dai mun yi ta kiran wayar ta domin mu ji ta bakin ta, amma dai ba mu same ta ba, domin kuwa duk wayoyin ta a kashe su ke, kuma duk wani makusancin ta mu ka tambaya, babu wani cikakken labarin ta da mu ka samu.
A ‘yan kwanakin nan dai an fara ganin jarumar ta na saka hotunan ta a shafukan ta na Soshiyal Midiya, kan haka ne ma sai mu ka gwada kiran wayar ta, kuma a shekaran jiya Lahadi bayan shan ruwa mun same ta a wayar, inda wakilin mu ya yi mata tambaya dangane da halin da ta ke ciki tsawon lokaci da ba a ganin ta.
Jarumar ta amsa da cewar.
“Gaskiya na yi rashin lafiya ne na tsawon lokaci shi ya sa ba a gani na, domin ko daga waya ma ba na yi, saboda ban san wanda zai kira ni ba, domin haka sai na kashe waya ta, amma dai a yanzu Alhamdulillah, na samu sauki na koma daidai”.
Mun tambaye ta ko a yanzu a ina take tun da ta samu sauki?
Sai ta ce “Yanzu ina gida garin mu Zuru, tun da yanzu ai babu wani abu da a ke yi, saboda a na zaman gida, domin haka yanzu ina gida ne da zama”.
Mun tambaye ta ko wacce irin cuta ce ta same ta?
Sai ta ce “To ai ka kira ni ne domin mu gaisa bari nan gaba zan kira ka sai na fada maka”. A cewar Zpreety.
To sai dai har zuwa lokacin da mu ka hada wannan labarin ba ta kirawo wakilin na mu ba, kuma mun yi ta kiran ta ba mu same ta ba, domin haka nan gaba idan mun ji daga gare ta za ku ji irin rashin lafiyar da ta sha fama da ita.
#Fimmagazine
Enter your comment…Allah ya karamaki lafiya ya kareki daga sherin makiya zulaihat zeeprty