Kannywood

Abinda Ya Hana Aure Na Da Adam A Zango – Jaruma Asiya MaiKyau

Advertisment

ASIYA Ahmad ta na daga cikin matasan jarumai mata da su ka yi fice a Kannywood. Jarumar, wadda ake yi wa laƙabi da Asiya Maikyau, ƙanwa ce ga fitacciyar ‘yar wasan nan Samira Ahmad.

Ya zuwa yanzu, Asiya ta samu kamar shekara biyar da fara yin aktin. Kuma ta shigo ne da ƙafar dama, saboda a lokacin da ta fara an yi wasoson ta.

Hakan bai rasa nasaba da cewa da gaske mai kyau ce, santala, doguwa, wato dai son kowa ƙin wanda ya rasa.

Haka kuma ga shi ta yi sabo da yawancin ‘yan fim saboda yayar ta Samira da mijin yayar a lokacin da ta shigo, wato fitaccen jarumi kuma mawaƙi, T.Y. Shaban. ‘Yan fim da dama na zuwa gidan su.

Bugu da ƙari, Asiya ta yi iya aktin ƙwarai da gaske, sannan ta shigo a daidai lokacin da furodusoshi da daraktoci su ke buƙatar matasan jarumai mata irin ta.

Waɗannan dalilai su ne su ka sa duk wanda zai saka Asiya a fim, to za ka taras a matsayin tauraruwar fim ɗin ya ke saka ta, wato mai jan fim ɗin.

Sai dai a hasashen da mujallar Fim ta yi, jarumar ta shigo Kannywood ne a daidai lokacin da harkar fim ta fara yin ƙasa. Hakan ya rage mata tashin gwauron zabon da ta fara yi, domin ba da jimawa ba aka shiga wani yanayi inda shirya fim sai wane da wane.

Idan masu karatun mu za su iya tunawa, mun taɓa bayyana maku a ‘yan shekarun baya cewa Asiya Ahmad budurwar fitaccen jarumi kuma mawaƙi Adam A. Zango ce. Abin nasu ma sai da ya rage kaɗan a ƙulla auren su, amma sai bai yiwu ba.

MUKHTAR YAKUBU na mujallar Fim ya tattauna da Asiya Maikyau don jin tarihin ta, da yadda aka yi ta zama ‘yar fim, da batun yadda Zango ya so ya aure ta. A ƙarshe, ta faɗa mana abin da ya fi damun ta game da ‘yan fim, har ta ba su wata shawara.

Ga yadda hirar ta kasance:

FIM: Da farko, ki fara da ba mu tarihin rayuwar ki a taƙaice.

ASIYA AHMAD: To ni dai suna na Asiya Ahmad, kuma an haife ni ne a garin Kano a shekarar 1994. Kuma na yi makarantar firamare a Giginyu, na yi sakandare a Da’awa.

FIM: Ya aka yi ki ka samu kan ki a cikin harkar fim?

ASIYA: Tun ina ƙarama ni na ke da sha’awar yin aktin, shi ya sa ma na ke tsayawa a gaban madubi ina gwada yadda ake yin aktin ina gani saboda abin ya na burge ni. Don haka sai na ke kallon kai na a matsayin jaruma!

To da na taso kuma sai na samu yaya ta, Samira, ta na yi. To babu yadda za a yi a ce ita ta na yi ni ma ina yi, dole sai ta matsa ni ma na samu na shiga.

To kuma da ta yi aure ka ga babu damar ta yi fim ɗin haka, sai na fara yi. Kuma alhamdu lillahi ko da na fara sai ya zama abin ya zo mini da sa’a.

Don haka a yanzu na cimma buri na, na zama jaruma.

FIM: Shi laƙabin ‘Maikyau’, ya aka yi ki ka same shi?

ASIYA: To sunan Maikyau da ka ji ana cewa Asiya Maikyau, na same shi ne tun daga fim ɗin da na yi na farko. Sunan sa ‘Mai Kyau’. A nan na samu wannan sunan, wanda kuma a yanzu ina jin fim ɗin zai kai shekaru biyar.

Kuma abin alfahari, daga fara fim ɗi na zuwa yanzu, duk da dai ba zan ce na fito a finafinai da yawa ba, amma waɗanda na fita za su kai wajen ashirin, don ina tuna wasu daga cikin su, kamar wanda na fito na farko, ‘Mai Kyau’, ‘Ranar Aure’, ‘Gida ‘Uku’, ‘Yankan Baya’, ‘Ƙanwa Ta’, da dai sauran su.

Kuma abin da ya fi burge ni shi ne duk finafinan da na ke fitowa ni ce na ke jan fim ɗin, wato jarumar fim ɗin.

FIM: Shin ko kin samu matsala a shigar ki harkar fim?

ASIYA: A gaskiya zan iya cewa ban samu matsala ba domin tun kafin na shiga harkar fim ɗin duk wani jarumi ya san ni na san shi, saboda su na zuwa gidan mu, don haka babu wata matsala da na samu, saboda na saba da su.

FIM: To yanzu da yake kin zama jaruma, wanne buri ki ke da shi?

ASIYA: To ni dai kusan zan iya cewa buri na ya cika, domin a yanzu duk inda na shiga an san ni a matsayin jaruma.

Wasu wuraren ma da ban isa na shiga ba, amma a matsayi na na jarumar da duniya ta sani sai na shiga har ma na shigar da wani.

FIM: A yanzu wanne abu ki ka saka a gaba da ki ke so ki cimma nan gaba?

ASIYA: A yanzu dai burin da na sa a gaba shi ne ina ci gaba da karatu, domin a baya ba n

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button