Yadda ‘yan fim su ka yi rashin iyayen su a mace-macen da a ka yi
A yanzu dai za a iya cewa jama’ar garin Kano da kewaye sun samu kan su a cikin wata Annoba ta yawan mace-mace da a ke yi babu dare babu rana, inda a cikin makon da ya gabata ne rahotonni ke nuni da cewa, mutane da dama sun rasu a cikin jihar babu adadi duk da a cikin kwanaki uku zuwa hudu mutane kusan sama da 300 ne su ka rasa rayukan su a wani harsashe da a ka yi, duk da hukumar lafiya ta jihar Kano ta musanta hakan, wanda kuma abun ya ci baga har zuwa lokacin da mu ke hada wannan labarin, wanda a na ta samun ci gaba da rasa rayuka, musamman da manyan mutane wanda shekarun su ya kai daga 60 zuwa sama.
Ko a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, an samu irin wannan mace-macen, inda a cikin makon da ya gabata ne wasu ‘yan fim sun yi rashin iyayen su.
A ranar 22 ga watan nan na Afrilu, mahaifin fitacciyar jaruma, Sadiya Gyale ya rasu, wanda a ka yi jana’izar sa a ranar 23 ga watan. Kuma a ranar dai ta 23/4 /2020 mahaifin fitaccen jarumin barkwanci, Ali Artwork, Allah ya yi masa rasuwa. Ko a makon da ya gabata ne, Allah ya yi wa mahaifiyar fitaccen mawaki, Ado Isah Gwanja rasuwa.
A ranar 26/4/2020 kuwa mun tashi da samun rasuwar mahaifin, Furodusa kuma jarumi, Tahir A Tahir rasuwa, yayin da shi ma jarumi Aminu Ilu Dambazau, Allah ya yi wa kanen mahaifin sa rasuwa, duka dai a wannan rana ta 26/4/2020. Baya ga haka, sai ga wani labarin kwatsam na rasuwar abokiyar zaman mahaifiyr darakta, Kamal S Alkali.
Da fatan Allah ya ji kan musulmai ya bai wa iyalai da ‘yan uwa hakurin jure rashin da a ka yi amin.